JIGAWA: Iyalai sun nuna damuwar jinkirin gurfanar da masu garkuwa da mahaifiyar su kotu

0

Iyalan da suka biya diyyar naira milyan biyar kafin masu garkuwa su saki mahaifiyar su, sun nuna damuwa dangane da jan-kafa da kuma jinkirin gurfanar da wadanda ake zargin su ne suka yi garkuwar a kotu.

An dai kama mutane shida da ake zargi da hannu a wannan garkuwa da aka yi a Jihar Jigawa.

Babban dan matar mai suna Abdullahi Muhammad, ya ce an sace mahaifiyar su a gidan ta cikin watan Yuni, kuma ‘yan sanda sun kama mutane shida da ake zargi. Amma har yau ba a gurfanar da su kotu ba.

Ya nuna cewa sun fara tsoron cewa wasu ‘yan siyasa ne jihar da ke da kusanci da wadanda aka kama din ke ta kokarin danne maganar kai su kotu.

Wata takardar bayani da ‘yan sanda suka buga, wadda wakilin PREMIUM TIMES ya gani da idon sa, ta nuna cewa wadanda suka yi garkuwa da gyatumar sun tattauna karbar diyyar naira milyan 5 ta wata lambar waya: 09054170931, tare da Muhammadu, domin ya biya kudin su saki mahaifiyar sa mai suna Lubabatu.

Takardar mai lamba JSX No. SARS/21/2019, an aika ta ne bayan kammala bincike ga Ofishin Daraktan Shigar da Kararraki Kotu na Jihar Jigawa a ranar 18 Ga Yuli, domin ya gurfanar da wadanda ake zargin Kotu.

Jami’an ‘yan sanda a cikin takardar sun nuna cewa binciken su ya tabbatar da cewa Muhammad dan wacce aka sace din ya biya kudin diyya, inda ya aiki wani direban sa mai suna Aliyu da kudin ya kai wa masu garkuwar a dajin hanyar Gumel zuwa Malam Madori, cikin Jihar Jigawa.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa wanda ya je ya karbi kudin wani Bafulatani ne wanda ke sanye da kayan sojoji.

Sannan kuma jami’an ‘yan sanda sun bi salsalar bincike, inda suka gano cewa wani malamin makaranta a Malam Madori ne ke da wannan lamba wadda aka masu garkuwa suka yi amfani da ita suka karbi kudin diyya a hannun dan wadda aka yi garkuwar da ita.

Wanda ke da wayar mai suna Ahmed Isa, an tabbatar da ya shaida wa jami’an tsaro yadda suka yi garkuwa da matar mai tsananin shekaru da dama.

Ya kuma shaida cewa gungun na su daga garuruwa daban-daban suka fito, kamar daga Kananan Hukumomin Malam Madori, Kaugama, Maigatari duk a cikin Jihar Jigawa.

Sannan kuma ‘yan sanda sun ci gaba da bayyana yadda Isa ya fallasa cewa an sallame shi naira 500,000 daga cikin naira milyan 5 da aka biya su diyya.

Ahmed Isa, Auwalu Usman, Munkaila Ahmed, Babangida Musa, Usman Hassan, Ahmed Hassan.

YADDA SUKA AMSA LAIFIN SU

A cikin takardar da ‘yan sanda suka gabatar wa Ofishin Daraktan Gurfanar da Masu Laifi Kotu na Jihar Jihar Jigawa, sun shawarci a maka su shidan kotu tare da tuhumar su da laifin hadin baki su kulla sata, shiga gidan mutane ba da izni ba, fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Wadanda aka nemi a gurfanar din sun hada da: Ahmed Isa, Auwalu Usman, Munkaila Ahmed, Babangida Musa, Usman Hassan, Ahmed Hassan.

Sauran wadanda ake nema amma suka arce, har yau babu labari, sun hada da: Danfulani, Musa Kabiru, Adamu Ya’u da kuma Bakoji Yusuf. ‘Yan sanda sun ce duk za a iya hada wadanda ake zargi din gaba dayan su a tuhume su lokaci daya, a karkashin Dokar Najeriya, Sashe na 96,343,296 da 271 na dokar aikata manyan laifuka.

ABIN DA YA HANA MU GURFANAR DA SU KOTU

Daraktan Gabatar da Kararraki Kotu na Jihar Jigawa, a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar, mai suna Musa Imam, ya bayyana dalilin jinkirin gurfanar da wadanda ake zargin da jinkirin da su ‘yan sanda suka yi wajen kammala binciken su da kuma dogon hutun watanni biyu da alkalai suka tafi, wand aba su dade da dawowa ba.

Ya ce ai cikin makon da ya gabata ne alkalai suka koma kotuna daga dogon hutun da suka tafi.

Daga nan ya bayyana cewa dama a al’adance babu yadda za a yi a gabatar da wanda ko wadanda ake tuhuma a kotu a lokacin da alkalai ke hutun su.

Sannan kuma daraktan ya karyata ji-ta-ji-tar cewa wai wasu manyan ‘yan siyasar jihar ne ke kokarin a saki wadanda ake zargin ta hanyar kamun-kafa da ofishin shi daraktan kan sa.

An yi zargin cewa wadanda aka kama din duk ‘yan jagaliyar siyasar wadancan manyan ‘yan siyasa ne.

Amma kuma Imam ya ce ba haka ba ne, ofishin sa ya karbi wani babban kundi mai dauke da tulin bayanan binciken da ‘yan sanda suka yi dangane da garkuwar, wanda kuma a hakikanin gaskiya inji shi, ya na bukatar nazari a tsanake saboda yawan sa, kafin ofishin sa ya bayar da shawarar yadda za a gurfanar da su, kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce ya na fatan cikin makon mai zuwa za su kammala dukkan nazarin da za su yi a kan batun domin bada shawarar yadda za a gurfanar da su.

Share.

game da Author