JIGAWA: An kori dan sandan da ke dibga sata kamar gafiya

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta bayyana wa PREMIUM TIMES korar wani kurtun dan sanda wanda sata za zame masa jini tamkar burgu.

Kwamishinan ’Yan Sanda ya bayyana cewa korarren barawon dan sandan mai suna Abdullahi Yusuf, ya na dibga sata ne ba-ji-ba-gani tare da daurin gindin mahaifin sa, wanda tsohon dan sanda ne.

An damke shi bayan ya saci talabijin da kuma wasu takalma da ba a fadi adadin ko guda nawa ba ne.

Kwamishinan ’Yan Sanda Sale Senchi, ya ce: “Wajibin kowane dan sanda ne ya kasance mai kyakkyawan halaye nagari, kuma abin koyi, shi ya sa aka ba shi amanar kare rayuka da lafiya da dukiyoyin jama’a.

“Saboda haka Rundunar ’Yan Sandan Jigawa ba za ta taba kyale duk wani jami’in ta da ke kokarin zubar mata da mutunci ba, ko zubar wa aikin dan sanda da mutunci ba.

Senchi ya ce dan sandan wanda aka kora sata ta zame masa jiki, tun farkon shigar sa aikin dan sanda ya ke dibga sata, bai daina ba.

“A baya ya taba shafe watanni hudu a tsare a ofishin CID a matsayin hukuncin wata sata da ya shirga.”

Sati biyu bayan sako shi ne kuma aka sake kama shi ya saci talbijin, daga nan ne kawai aka yanke hukuncin korar sa daga aikin dan sanda. Haka PREMIUM TIMES ta samu labari.

Tun da farko, wanda aka yi wa satar talbijin din mai suna Muktar Yunusa, da ke Unguwar Sarki a cikin garin Dutse, ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa korarren dan sandan ya shiga gidan sa da rana ya yi masa sata, ta hanyar yin amfani da makullai biyar daban-daban.

“Lokacin da ya fito niki-niki dauke da talbijin da ‘remote contro’ da takalma, sai na tambaye shi ina zai kai su? Sai ya nuna min ai ya san maigidan shi ya aike shi, bai san ni ne maigidan ba.

“Daga nan sai na kira makwabta na, muka yi cacukui da shi zuwa ofishin ‘yan sanda.” Inji Yunusa, wanda aka dibga wa sata.

Share.

game da Author