Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta bayyana kama wani kofur din soja da daurin tabar wiwi 169, a cikin Karamar Hukumar Ringim.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Jigawa, Bala Sanchi ne ya bayyana haka da kan sa a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, a yau Laraba.
Sojan dai kamar yadda Sanchi ya bayyana, an tura shi ne domin yaki da Boko Haram, amma ya tsere tun watanni bakwai da suka gabata.
Kwamishinan ‘yan sanda Sanchi ya yi bayanin cewa an kama wanda ake zargin ne tun a ranar 17 Ga Satumba, wajen karfe 2:30 na rana.
Ya ce ‘yan sandan ‘Operation Puff Adder’ ne suka damke shi a kan titin Sankara zuwa Amaguwa, cikin Karamar Hukumar Ringim.
An kama shi tare da mota kirar Toyota Camry, mai lamba KTU 833 DK.
Ya ce an kama shi bayan da jami’an ‘yan sanda suka samu labarin wani hatsari da motar ta yi.
“Yayin da suka isa wurin da motar ta yi hatsari, sun samu motar da ta yi hatsarin, mai lamba KTU 833 DK, samfurin Toyota Camry.
“Da suka yi tambaya, sai suka samu labarin cewa wani jami’in soja ne mai sanye da kakin soja ya tuko motar.
“Da jami’an mu suka tsananta bincike a cikin motar, sun samu daurin tabar wiwi har 169.
“Wanda suka kama din a cikin kayan sojoji, kofur ne mai suna Muzambilu Abdullahi, da aka tura yaki da Boko Haram, amma ya gudu tun watanni bakwai da suka gabata.
Da aka tsananta binciken sojan, ya ce wani mai suna Alhaji Abubakar daga Lokoja ne ya dauko shi, domin ya yi masa rakiya zuwa Maigatari, a Jihar Jigawa.
Ya ce bai san Alhaji Abdullahi na dauke da damman wiwi a cikin motar ba.
Da aka tambaye shi inda Alhajin ya ke, sai sojan ya ce ya gudu bayan da motar ta yi hatsari.
Kwamishinan ‘yan sanda ya kara da cewa an kuma kama wasu mutane kusa da motar, wadanda bayan bincike suka tabbatar da cewa su ne dillalan da ke sayen tabar wiwi din da aka kama.