Jawo Hankalin Shugaban Kasa Da Jami’an Tsaron Najeriya: Gwamnan Kano Yana Neman Cinnawa Jihar Wuta! Daga Imam Murtadha Muhammad

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Ya Mai girma Shugaban Kasar Najeriya, Alhaji Muhammadu Buhari, ina fatan wannan sako na wa zai same ka cikin koshin lafiya da amincin Allah? Allah yasa, amin.

Ya mai girma Shugaban Kasa da jami’an tsaron Najeriya, bayan gaisuwa da girmamawa, wannan sako ne zuwa ga reku, domin sanar da ku abin da yake faruwa a Jihar Kano, domin ka da wani abu na rashin tsaro ya faru kuce ba’a sanar da ku ba, ko kuma kuce ba ku da labari. Allah ya kiyaye, ya zaunar da mu lafiya, amin.

Ya mai girma Shugaban Kasa, labari ya iso muna ta majiya mai karfi kuma mai tushe, cewa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gama shiri tsaf domin tsige Sarki mai daraja, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II. Labari ya iso muna cewa, Gwamna za ya umurci Mai Martaba Sarki da ya koma garin Bichi, ko ya bar Sarautar gaba daya. Idan kuma ya ki zai cire shi daga Sarautar.

Ya mai girma Shugaban Kasa, Allah shine shaida, Allah ya kiyaye, wallahi ina mai ji muna tsoron tashin gobara a Jihar Kano, muna jin tsoron tashin wutar da za ta zama sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa na bayin Allah, talakawa. Wadanda a matsayin su na ‘yan Najeriya, kayi alkawari, kuma kayi rantsuwar kare rayukan su da dukiyoyin su.

Ya mai girma Shugaban Kasa, ina jin tsoron jawo abun da zai zama sanadiyyar ruguza kadarori marasa iyaka, na bayin Allah, talakawan ka.

Ya mai girma Shugaban Kasa, ina tsoron jawo barnar da, ba za ta tsaya a Jihar Kano kawai ba, a’a, barnar da za ta mamaye Arewacin Najeriya da kasar nan baki daya.

Ya mai girma Shugaban Kasa, ina jin tsoron tayar da wutar da za ta yi sanadiyyar ruguza wannan dimokradiyyar da muke tinkaho da ita.

Ya mai girma Shugaban Kasa, mutanen Jihar Kano cike suke da fushin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, saboda ire-iren halayen sa da dabi’un sa na musgunawa jama’ah; halayen sa da irin salon mulkin sa na jefa kanawa cikin talauci, rashin aikin yi, tare da hali na rashin mutunci da yake nuna masu kullum. Ya mayar da Jihar kamar ba Jihar Kano da aka sani ba!

Ya mai girma Shugaban Kasa, Mawakan Gwamna Ganduje za su yi waka, su zagi Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, su ci mutuncin sa, su yi batanci zuwa ga re shi, su fadi abunda suke so akan sa, Gwamna yayi masu kyauta ta alfarma, yayi masu alkhairi shi da ‘yan bangar siyasar sa. Amma da zaran mawakan Mai Martaba Sarki sun yi waka, ba domin su zagi kowa ko su ci mutuncin kowa ba, a’a, sai don su kare Martabar Sarki, nan ta ke sai Gwamna yasa a kama su, aci masu mutunci, a kai su gidan yari a daure. Har yau mun kasa fahimtar wannan wane irin hukunci ne! A yanzu haka, Allah ne kadai yasan iyakar ‘ya ‘yan talakawan da Gwamna Ganduje yasa aka tsare.

Duk da wannan, mutanen Jihar Kano sun danne fushin su, suna zaune lafiya, suna ta addu’ar Allah ya kare su da kuma Arewacin Najeriya da kasar nan baki daya daga afkawa cikin irin abubuwan da suke faruwa na ta’addanci da rashin tsaro a wasu wurare. Allah ya kiyaye, amin.

Ya mai girma Shugaban Kasa, dukkanin mu mun yi imani da Allah cewa, ana yin mulki ne domin hada kan al’ummah da ciyar da su gaba. Mun san ana yin siyasa ne domin kawo wa jama’ah alkhairi da amfani. Mun san ana yin Shugabanci ne domin kare dukkan sharri da zai afkawa al’ummah. Amma a Jihar Kano gaskiya ba haka abun yake ba. Domin siyasar Jihar Kano a halin yanzu ta rarraba kan al’ummah, ta tarwatsa su, sannan kuma tana neman jefa Jihar cikin babbar damuwa idan ba’a dauki kwakkwaran mataki ba. Allah ya kiyaye, amin.

Ya mai girma Shugaban Kasa, muna masu sanar da kai cewa, tura fa tana neman kai wa ga bango! Domin Gwamna Ganduje a halin yanzu ba shi da tunani illa ya jawo rigima, ko ya jefa Jihar Kano cikin tashin hankalin da Allah ne kadai yasan karshen sa.

Ya mai girma Shugaban Kasa, muna rokon da ka ja wa Gwamna Ganduje kunne, ka sa masa linzami, kafin ya jawo muna masifar da ba mu san a inda zata tsaya ba! Allah ya tsare kuma ya sawwake, amin.

Haka nan ma muna roko ga hukommin tsaron kasar nan, da su sa kaimi, su tabbata sun gargadi Gwamna Ganduje. Kuma su nuna masa cewa, yayi hankali kar ya jefa Jihar Kano cikin masifa. Allah ya kiyaye, amin.

Mun san duk dai duniya tana kallo, kuma tana ji, kuma tana sane da cin mutunci da tsokana da wulakanci kala-kala, iri-iri, daban-daban da Gwamna Ganduje yake nunawa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.

Kwanan nan, don rainin hankali, Gwamna Ganduje yasa aka jera hotunan wasu hakimai guda hudu tare da hoton Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, a dakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnatin Jihar Kano, ba don komai ba sai don tsokana da neman tayar da hankalin Kanawa da aka sani da hakuri da son zama lafiya. A da hoton Mai Martaba Sarki ne kawai a wurin, amma yanzu sai aka jera hotunan wadannan hakimai da na Sarki, kuma aka mayar da hoton Mai Martaba Sarki a karshe da nufin cin mutuncin Sarki! Sun manta da cewa, duk wanda Allah ya rufa wa asiri, kuma yayi masa sutura, to fa babu mai iya yi masa komai!

Duk wasu mutane masu mutunci da daraja, tun daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, har zuwa manyan Sarakunan mu na Arewa, har zuwa babban Dan kasuwar Afirika, mai daraja Alhaji Aliko Dangote da Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i da mai girma Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, sun sa baki a cikin wannan magana, amma Gwamna Ganduje yayi biris, yayi kunnen uwar shegu da duk maganganun su, yaci gaba da bita-da-kullin da ya saba yiwa Mai Martaba Sarki. Sai kace ba Musulmi ba, sai kace ba Dan Arewa ba, sai kace ba Dan Kano ba!

Duk duniya ta shaida, Mai Martaba Sarkin Kano yayi hakuri iya hakuri, amma wannan Gwamna, sam, har yanzu bai dai na cin mutuncin masarautar Kano ba mai dimbin tarihi, wadda tana daya daga cikin masarautun da Shehu Usman Dan Fodiyo yayi jihadi domin kafawa.

Ya mai girma Shugaban Kasa, kwanan nan aka yada wasu rade-radi, cewa fadar Shugaban Kasa ta samu matsala ta rashin jituwa tsakanin ta da mataimakin Shugaban Kasa, wato Farfesa Yemi Osinbajo, amma nan ta ke, wallahi, sai dukkan Sarakunan kasar yarbawa suka fara shirye-shirye, tare da kokarin daukar mataki domin su kare Dan uwan su. ‘Yan siyasar kudu har kullun, suna kallon Sarakunan su da mutunci, suna girmama su, suna ganin darajar su. Amma shin me yasa wasu ‘yan siyasar mu na Arewa ba su girmama Sarakunan mu ne, kuma ba su san darajar su ba?

Ya mai girma Shugaban Kasa, muna rokon da ka sa baki cikin wannan badakala, ka ja kunnen Gwamna Ganduje. Ya kamata ya mayar da hankalin sa wurin ci gaban Jihar Kano da Kanawa baki daya, ba kawai yayi ta kashe dukiyar Jihar Kano wurin fada da Mai Martaba Sarki ba!

Ya mai girma Shugaban Kasa, wallahi, ka sani, Kanawa basu jin dadin wannan abun da Gwamna Ganduje yake yiwa Mai Martaba Sarki. Sun yi fushi, sun fusata, sun harzuka matuka! Don haka don Allah muna rokon da ka sa baki domin kauce wa fitina da tashin hankalin da ke neman faruwa a Jihar Kano!

Muna rokon Allah ya zaunar da Jihar Kano lafiya da Najeriya baki daya. Allah ya gina muna katangar karfe, kuma ya shiga tsakanin mutanen Jihar Kano, masu son zaman lafiya, masu kaunar Sarkin su, daga mugun tanadin dukkan wani mutum makiyin zaman lafiya, amin.

Wassalamu Alaikum,

Daga Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad, ya rubuto ne daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma: 08038289761.

Share.

game da Author