Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa Maryam Yahaya ta karyata rade-radin da ya karade shafunan sada zumunta na Facebook cewa wai ta riga mu gidan gaskiya.
Maryam ta karyata wannan rade-radi ta na mai cewa sharri ne kawai amma babu abin da ya taba lafiyarta ballantana ma ace wai ta mutu.
Da take karyata hakan a shafinta na Instagram, tace ita ko shafin Facebook bata da shi da a nan ne aka fi yada wannan karya na rasuwar ta.
” Ina nan daram ban mutu ba kuma ma cikin koshin lafiya. Wadanda suke yada wai na mutu karya suke yi.
Maryam ta ce ta fito da kanta ne domin ta shaida wa duniya cewa karya ake yi.
” Ni fa ko shafin Facebook bani da shi da a nan ne ake ta rubutawa wai na mutu. Duk wani shafi na Facebook da kuka gani da suna na ko hotona, ba nawa bane.
A karshe ta godewa masoyanta da suka rika nemanta tun bayan karanta wannan labari na rasuwarta.
Maryam na daga cikin jaruman da suka taka rawar gani a shahararren fim dinnan wanda jarumi Ali Nuhu ya shirya mai suna ‘Mansoor’.
Idan ba a manta ba, shima Adam Zango ya taba yin irin wannan kuka a shafinsa na Instagram, inda ya ce wasu na yadawa wai yayi hatsari a hanyar sa na dawowa daga Kasar Nijar har ma ya rasu.
Zango ya karyata haka.