Na dade ina nazari akan wannan lamarin da yake faruwa a cikin al’umma wanda a dan nawa fahimtar ina ganin kaman hakan ba shine mafita ba. Sai kaga mutum duk abinda ya fara yace Buhari, duk abinda yayi yace Buhari, akasarin abubuwan da kuma suke jinginawa Buharin ba abin kirki bane. Baza kaga mutum ya aikata abin kirki ya kira sunan Buhari ba ko da kuwa mutum a wannan lokacin ya samu abin.

A duk lokacin da mutum ya tsinci kansa cikin wata hali, walwala ne ko masifa, ya kamata sunan ALLAH ne zai dinga zuwa bakinsa ba sunan wani dan adam wanda a tunaninsa ta sanadiyar wannan ya tsinci kansa cikin wannan halin ba. Idan cikin walwala kake kai kullum abinda zai fito daga bakinka ALLAH mun gode maka da wannan budin ka karama mana masu albarka. Idan ko masifa ta sameka, Allah kafimu sanin halin da muke ciki ka fiddamu daga wannan halin. Ina ganin wannan shine abinda zai taimakemu.
Amma kawai mutane sun manta da sunan ALLAH a bakunansu sai sunan Buhari, mai sana’a Buhari, zauna gari banza Buhari, mai samu daman marowaci ne idan kayi magana yace Buhari, wanda bai samu yace Buhari. Zaka ga mutum a baya baida ko naira amma yanzun ALLAH ya bude masa hanyan samu gashi kana ganin yana abubuwan kudi fiye da shekaru bakwai baya idan ana hira aka kawo maganar kudi sai kaji yace Buhari saboda wannan kalma mutane sun maida ita ta zama yayi (abin fada).
To wannan fa shine halin da wadansu al’umma suka makara, mutum zai makara gurin kiran sunan Buhari a madadin sunan ALLAH, har ALLAH ya dauki ransa da sunan Buhari a bakinka ka manta da sunan ALLAH da ya dace ka mutu dashi a bakinka.
Saboda haka mutane ya kamata muyi hatara da wannan dabi’a. A ko wace hali ka same kanka ALLAH zaka kira ko da kuwa wannan halin ta sanadiyar wani ka shigeta. Domin kuwa ba wani dan adam da zai fidda kai daga wannan halin ba da yardar ALLAH ba.
Yaa ALLAH ka kara mana imani, kasa mu mutum da imani da kyawawan ayyuka da kuma kiran sunanka a bakinmu.
Yaa ALLAH ka bamu zaman lafiya a Nigeriya dama duniya gaba ki daya.
Yaa ALLAH ka bamu damina mai albarka.
Yaa ALLAH ka kara mana budi ta hanyan halal.
Yaa ALLAH kaba shuwagabanninmu ikon yi mana shugabanci nagari.
Amen.
Discussion about this post