HATTARA: A dai na bada aro ko amsar aron wayan cajin waya – BINCIKE

0

Kungiyar masana yin kutse da binciken kwakwaf a Komfuta da Wayoyi sun gargadi mutane da su daina bada aron wayoyin cajin Komfutan su da wayoyin su.

Charles Henderson da shine jagoran wannan kungiya ya bayyana cewa akwai wasu da ke amfani da irin wannan fasaha na binciken kwakwaf da zakulo bayanan mutane ta hanyar saka wani irin fasaha a cikin wayan cajin wayoyi.

” Da zaran sun baka aron wannan waya don kayi caji sai ya tattaro duka bayanan ka ya tura musu. daga nan sai su bankado duka abubuwan da suke bukata naka domin yin amfani da su.

Henderson ya ce a dalilin haka masu kutse kan samu damar yi wa mutum sata ko kuma zakulo bayanan sirri masu mahimmanci daga wayan cajan baka ma sani ba.

“Yanzu dai wannan fasaha bata riga ta karade duniya ba amma masu yi wa mutane kutse da binciken kwakwaf sun bude faifai haka kuma suna ci gaba da kirkiran irin wadannan wayoyi domin kwakulo bayanan mutane.

Sannan kuma a ci gaba da gargadi ya Henderson yayi, yace, a rika gujewa yin cajin waya a tashoshin jirgin sama ko kuma na kasa ko kuma inda kowa da kowa kan saka wayar cajin sa domin cajin waya a ko ina ne kuwa.

A karshe ya yi kira ga mutane da su rika siyan sabon wayan cajin waya idan nasu ya bace ko kuma suka manta da shi a wani wuri.

Share.

game da Author