Hassadar Kasa-da-Kasa Ce Ta Saka ‘Yan Kasar Afrika Ta Kudu Illata ‘Yan Najeriya, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Mun yi matikar mamaki yadda ‘yan kasar Afrika ta kudu suke illata ‘yan uwanmu a kasarsu. A shekarar 1994, Najeriya tana cikin kasashen da suka yi kokari wajen kawo karshen tsangwamar ‘yan kasar da fararen fata suke yi.

Mun yi musu rana sun yi mana dare, mai ‘yan kasarmu suka yi da suka cancanci wannan zaluncin?

Amma ban yi mamaki ba domin bayahudiyar hassada ce ta kawo hakan saboda matsayin da Najeriya take dashi a cikin jerin sunayen kasashe masu tattalin arziki a Afika.

Duk da matsaloli da muke ciki, har yanzu kasar Afrika ta kudu ta kasa kyeremu, tun lokacin Goodluck Jonathan ake bugawa da ita har yau. Ko a sabuwar kididdiga da akayi Najeriya tana gaba da ita.

Tsakanin Najeriya da Afrika ta kudu duk ‘common wealth nations ne’ ma’ana dukkansu rainon kasar ingila ne.

Madadin su samu kyakykyawar alaka ta kasa-da-kasa amma ‘yan Najeriya sun zama abubuwan muzgunawa da zubar da jini a can kasar.

Idan haka suka fahimci alaqar kasa-da-kasa, babu shakka sun yi kuskure saboda babu kasar da zata iya rayuwa ita kadai, sai ta marabci wasu ‘yan kasar zata cigaba.

Babu shakka, duk da zargin cin hanci da rashawa a tsakanin ‘yan Najeriya amma Allah yasa musu albarka, hannunsu yana samar da arziki duk duniya don haka cin mutuncinsu zai jawowa Afrika ta kudu matsala a tattalin arzikinta.

Najeriya cibiyar kasuwanci ce don muna da yawa, samun matsala da ita zai shafi manyan kasuwancin Afrika ta kudu a Najeriya. Irinsu MTN, Shoprite, DSTV, Gotv, Stanbic IBTC da sauransu.

Kauracewa wadannan kasuwancin zai girgiza kasar Afrika ta kudu sosai, waye yayi rashi kenan? Wannan ya faru da manyan kasashe a duniya irinsu Denmark kuma sun ji jiki, ballanta kasa kamar Afrika ta kudu.

Akwai rashin wayewar kai a wannan aikin nasu, duk da cewa kasar tana cikin kasashen da ba za a manta dasu ba a Afrika idan za a yi maganar tarihin yadda canje-canje ya samu a rayuwar dan Adam a Afrika.

Ina fatan ‘yan Najeriya zasu kauracewa kasar tunda abun ya faru ba sau daya ba, akwai alamomin hassada a ciki saboda meyasa abun ya tsaya akan iya ‘yan Najeriya kawai.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author