HARIN BOKO HARAM: An kashe sojoji bakwai, wasu bakwai sun bace a jihar Barno

0

Majiya daga rundunar Sojin Najeriya ya bayyana cewa sojoji bakwai sun mutu sannan wasu bakwai sun bace a wani hari da Boko Haram suka kai a jihar Barno.

Kamar yadda muka jiyo daga majiyar mu Boko Haram sun yi wa sojojin kwantar bauna ne a kauyen Madamari da misalin karfe 4:30 na yammacin Laraba a hanyarsu na komawa Maiduguri daga Gubio.

Bayanai sun nuna cewa kafin a kawo wa sojojin taimako Boko Haram sun kashe sojoji bakwai, wasu bakwai kuma sun bace sannan sun bankawa wata motar yaki dake cikin motocin jerin gwanon sojojin.

Wani babban jami’in sojin Najeriya ya ce ana zaton cewa Boko Haram ne suka dauke wadannan sojoji da suka bace.

Kamfanin dillancin labarai na ‘Reuters’ ta rawaito ranar Alhamis cewa sojoji bakwai ne Boko Haram suka kashe a harin ranar Laraba.

Hakan na nuna cewa sojoji bakwai din da rundunar sojin Najeriya ke tunanin an dauke su ne kila mutuwa suka yi.

Garin Madamari na daga cikin kauyukan da rundunar soji ta kwashe sojoji daga.

Idan ba a manta ba sojoji sun rage yawan barbaza sojoji a kauyukan jihar, sun tattara su a waje daya ne a yanki.

Sai dai yin haka ya kawo rudani inda mazauna ire-iren wadannan garuruwa ke kokawa game da haka, suna cewa an bar su da halin su.

Kakakin rundunar sojin Najeriya Sagir Musa bai amsa waya ba a lokacin da wakilin mu ya kira shi.

Share.

game da Author