Tun bayan sanar da karin harajin VAT da gwamnatin tarayya ta yi cewa nan ba da dadewa ba za a fara biyan harajin VAT da ada yana kashi 5% ne zuwa 7.5% mutanen Najeriya suka yi wa wannan shiri na gwamnati caa da tofa alabarkacin bakinsu game da haka.
Mutane sun koka cewa basu ga dalilin yin wannan Kari a wannan lokaci da ‘yan Najeriya ke fama da Yunwa da Talauci ba suna masu cewa idan hakan sam bai dace ba a wannan lokaci.
Mutane sun rika yi wa gwamnati nuni da cewa idan fa aka kara wannan haraji kayan masarufi za su karu matuka domin kuwa yan kasuwa suma za su yi fama da hauhawar farashin kayayyaki tun daga ‘inda suka siyowa zuwa kasuwannani.
Bayan haka wasu da dama na ganin wadannan haraji ana tara wa wasu ne dabam da ke jijjida su aljihun su amma ba wai za ayi wa ‘yan Najeriya aikin azo a gani bane dasu.
A daidai ana ta tunani yadda rayuwa zata kasance ne idan aka fara karbar wannan kudi na haraji sai kwatsam kuma gwamnati ta bujiro da wani sabon harajin.
Wannan karon harajin na kudin ka ne da ka wahala nema. Idan ka kai banki za a cire kudin haraji, idan zaka cira za a cire kudin haraji. Haraji ta ko ina babu kakkautawa.
Wannan sabon shiri da babban bankin Najeriya ta kirkiro ya tada wa mutane da dama hankali.
Wani dan kasuwa dake garin Kaduna ya rika sukar wadannan hariji da gwamnati ta ke ta kirkirowa batare da la’akari da yadda ake fama da kunci ba.
” Wallahi wannan haraji talaka ne zai wahala dashi domin da zaran sun fara aiki farashin komai zai hauhawa matuka. Farashin kayan abinci zai lula sama. Sannan kuma dama can idan aka lura samu ya karanta yanzu.
Yayi kira ga gwamnati da su rika yin sara suna duban bakin gatari kafin su kirkiro ire-iren abubuwa irin haka.
Mutane da dama sun ce idan abin yayi wuya, zasu koma yadda ake a zamanin da ne, kowa zai siyo asusun sa ya ajiye a karkashin gado. Dan abin da yake dashi ya ajie ya rika ci a hankali ba sai ya kai inda za arika zaftare masa gumin sa ba da sunan wai haraji.
Discussion about this post