HARAJI: UN ta shawarci Najeriya ta kakaba harajin kangayen gidaje

0

Wata jami’ar Majalisar Dinkin Duniya, mai suna Leilani Fartha, ta yi kira ga Najeriya da ta fito harajin da za ta kakaba ana biya wa kangayen gidajen da babu kowa a cikin su.

Leilani, wadda ita ce jami’ar rajin ’Yancin Samar da Wadatattun Gidaje, ta ce idan Najeriya ta fito da wannan haraji, zai rage kalubalen matsalar muhallin da ta ke fuskanta.

Ta yi wannan shawara ko kira ne a wurin wani taron ‘yan jarida a Abuja, inda ta nuna damuwa dangane da irin halin zaman kuncin da ‘yan Najeriya ke rayuwa ciki a wasu yankunan ‘share-wuri-zauna’ da ke gefen Abuja.

Leilani ta ce kashi 69 bisa 100 na al’ummar kasar nan duk suna zaune ne irin wadannan matsugunai wadanda da dama daga cikin su ba su da ababen jin dadin rayuwa na tilas, kamar ruwan sha da wuraren kula da lafiya.

“Sannan kuma babu tsaro, a kullum su na tunanin za a iya korar su daga inda su ke zaune.

“Kwanaki 10 da mu ka yi mu na bincike da nazari a Najeriya, ya nuna irin zaman kashin-dankalin da ake yi a kasar nan. Hakan ya fi karfi ne ma wajen nuna fifiko ko bambancin muhalli da wurin zama.

“Akwai matsalar karancin gidaje har milyan 22 da akalla ake bukata da gaggawa.

“A lokaci guda kuma sai kantama-kantama gine-gine ake ta yi a cikin birane, wadanda wasu ma kafin a yi ginin sai an tashi masu karamin karfi, an raba su da inda su ke.

“Irin wadannan gine-gine ba su cike gurabun bukatar muhalli. Da yawan su ma haka su ke kasancewa babu kowa a cikin su har tsawon shekaru da dama. Sun zama hanyar karkatar da kudade da harkalla kawai.” Inji Leilani.

Yayin da a gefe daya ta ke kiran gwamnati ta gaggauta shawo kan matsalar muhalli da kuncin talauci, a daya gefe kuma ta nemi a kafa dokar daina korar masu kananan karfi daga gidajen su.

Share.

game da Author