HARAJI: Bankin CBN ya zabga harajin ajiya da cirar kudi a bankuna

0

Tun daga yau Laraba, duk wani mai ajiyar kudi a banki zai fuskaci karin harajin ladar ajiya da cirar kudade a bankin da yake mu’amala da shi.

Wannan kakkausar sanarwa ta fito ne jiya Talata daga Babban Bankin Najeriya, CBN.

An aika wa dukkan bankunan kasar nan wannan sanarwa ce, wadda Daraktan Kula da Ajiyar Kudade na CBN, Sam Okojere ya sa wa hannu.

Sanarwar ta ce duk wanda ya kai ajiyar naira 500,000 abin da ya yi sama, za a caje shi kashi 3 bisa 100 na kudin da ya kai ajiya.

Shi kuma wanda zai cire ko ya kwashi naira 500,000 abin da ya yi sama, za a cire masa kashi 2 bisa 100 na adadin yawan kudin da aka zuba.

Sannan kuma za a cire harajin kashi 5 bisa 100 idan asusun ajiyar na kamfanoni ko masana’antu ne daga adadin kudin da za a cire, idan sun kai naira milyan 3 abin da ya yi sama.

Idan kuma ajiya aka kai banki, to za a cire ladar ajiya harajin kashi 3 bisa 100 na adadin kudaden, idan sun kai naira milyan 3 abin da ya yi sama.

Bankin CBN ya ce wannan karin da aka yi za a lafta shi ne a kan adadin kudaden da ake caji kafin wannan kari da aka yi.

Sai dai kuma sanarwar ta ce wannan kari zai shafi wadanda ke tu’ammali ko hada-hadar kudade a bankuna a garuruwan Lagos, Ogun, Kano, Abia, Anambra, Rivers da kuma Abuja ne kadai.

Idan ba a manta ba, cikin makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar karin harajin kayayyaki daga kashi 5 bisa 100 zuwa kashi 7.5 bisa 100.

Wannan ya jawo ka-ce-na-ce, har Majalisar Tarayya ta ce za ta kira Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed domin ta yi bayani.

Share.

game da Author