A cikin watanni shida kacal, gwamnatocin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomin sun kasshe naira tiriliyan 3.84.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kungiyar Bin Diddigin Masana’antu ta Najeriya, wato NEITI. Haka dai ta buga a cikin bayanin da ta wallafa na bin diddigin watannin da suka gabata na kwanan nan da ta fitar.
NEITI ta fitar da wannan rahoto ne jiya Lahadi a Abuja, inda kungiyar ta kara nuna cewa gwamnatin tarayya ta kashe naira tiriliyan 1.599. Sannan kuma jihohi 36 sun lashe naira tiriliyan 1.335, yayin da kananan hukumomi 774 suka kashe naira bilyan 792.
Sai dai kuma NEITI ta ce naira tiriliyan 3.84 da gamayyar gwamnatocin uku suka kashe a cikin watanni shida na farkon 2019, ba su kai yawan adadin da suka kashe a farkon watanni shida na shekarar 2018 ba.
NEITI ta ci gaba da da aikin ta na bin-diddigin kudaden da gwamnatocin suka kashe a watanni shidan farkon 2018 cewa sun kai naira tiriliyan 3.94.
A watanni shida na farkon shekarar 2017 kuwa, NEITI ta bi diddigin cewa naira tiriliyan 2.70 ne gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da kuma kananan hukumomi suka kashe, ko kuma a ce duk suka karba daga Hukumar Rarraba Kudade ga gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi.
Kakakin NEITI, Ogbonnaya Orji ne ya yi wannan karin haske.
Wannan rahoto ya ci gaba da yi wa kudaden shigar da gwamnatin tarayya ke samu filla-filla, tun daga na shekarun baya, har na cikin wannan shekara ta 2019.
Discussion about this post