Gwamnatin jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana cewa gwamnati ta kara horas da ma’aikatan kiwon lafiya 1,000 a jihar.
Masari ya fadi haka a taron inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana da aka yi a jihar a watan Agusta.
Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin kawo karshen karancin ma’aikatan kiwon lafiya da ake fama da shi a asibitocin jihar.
“ Gwamnati ta ware isassun kudade domin gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda daya a kowane mazaba dake jihar a Kasafin kudin wannan shekara.
Masari ya ce a taron za a bada magungunan tsutsan ciki na yara, Vitamin A, yi wa yara allurar rigakafi, rajistan haihuwa, gwajin cutar kanjamau musamman ga mata masu ciki, bada dabarun bada tazarar iyali kyauta.
A karshe babban sakataren ma’ikatar kiwon lafiya na jihar Katsina Kabir Mustapha ya yaba goyan bayan da kungiyoyin bada tallafi suka yi wajen inganta fannin kiwon lafiya jihar.
Mustapha ya yi kira ga maza da mata iyaye da su garzayo da ‘ya’yan su domin a yi musu rigakafi allurar rigakafi kyauta.