Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Barno Salisu Kwaya-Bura ya bayyana cewa gwamnati za ta gina manyan asibitoci uku domin kula da marasa lafiyan da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ba za su iya duba su ba.
Kwaya-Bura yace gwamnati ta yi haka ne domin samar da kiwon lafiya na gari ga mutanen jihar musamman mazaunan karkara.
Ya ce za a gina wadannan asibitoci ne a kananan hukumomin Bama, Monguno da Biu.
Kwaya-Bura yace gwamnati za ta gina makarantar koyon aikin likita domin samar da isassun ma’aikata a asibitocin dake jihar.
“Yin haka na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin samar da ababen more rayuwa ga mutanen jihar.
A karshe Kwaya-Bura ya jinjina wa kungiyar bada taimakon jinkai na ‘Red Cross’ kan yadda suke tallafa wa gwamnati wajen gyara asibitin kula da masu tabuwar hankali da karayan kashi a jihar.
Bayanai sun nuna cewa asibitin na da girman kula da marasa lafiya akalla 2,000 sannan kungiyar ‘Red Cross’ ta bada gudunmawar Naira miliyan 3.5 domin gyaran asibitin har ila yau.