Babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya Abdulaziz Abdullahi ya bayyana cewa gwamnati ta yi nasaran dakile yaduar cutar kurkunu dake kawo makanta wato ‘River Blindness’ a jihohi bakwai a kasarnan.
Wadannan jihohi kuwa sun hada da Filato, Nasarawa, Kaduna, Oyo, Kebbi, Zamfara da Bauchi.
Saboda wannan nasara da aka samu na dakile yaduwar cutar Abdullahi yace dama can mutane miliyan 4.2 ne ga gwamnati ke samar wa maganin cutar kyauta da yanzu ba a yi kuma saboda sauki da aka samu.
A dalilin haka, yanzu Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen da suka yi nasaran dakile yaduwar cutar a kasashen su.
A kwanakin baya ne Jami’in hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Gombe Danjuma Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ta raba maganin ‘Mectizan’ kyauta a kananan hukumomi 10 a jihar.
Mohammed yace gwamnati ta yi haka ne domin dakile yaduwar cutar kurkunu a wadannan kananan hukumomi dake jihar.
Akan kamu da cutar kurkunun dake sa makanta idan kudan da ke dauke da tsutsa da ake kira ‘Blackfly’ ya ciji mutu.
Wurin da kudan ya cija kan kumbura ya duri ruwa saboda tsutsan da ya shiga jikin mutum sannan ya ci gaba da girma.
Rashin cire wannan tsutsa kan sa ya kaiga shiga idon mutum wanda yake iya sa makanta ko kuma ya shanye kafan mutum.
Rahotanni sun nuna cewa mazauna karkara musamman wadanda ke zama a kusa da ruwa sun fi kamuwa da wannan cuta.