A tsakanin shekarar 2017 da 2018 gwamnatin Najeriya ta kashe akalla Naira biliyan 1.8 don ciyar da yara kanana dake fama da matsanancin yunwa a jihohi 18 dake kasar.
Shugaban sashen yaki da kawar da yunwa na ma’aikatar kiwon lafiya Chris Isokpunwu ya sanar da haka ranar Lahadi da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Isokpunwu ya bayyana cewa sakamakon binciken da ma’aikatar kiwon lafiya ta gudanar a 2017 ya nuna cewa jihohi 18 a kasar nan na fama da matsanancin yunwa.
Ya ce a dalilin haka gwamnati ta tsaro matakai tare da hada hannu da Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin ganin ta kawo karshen wannan matsala a Najeriya.
“A 2017 gwamnati ta ware Naira biliyan 1.8 domin samar da kula ga kananan yara dake fama da matsanancin yunwa a jihohin Anambara, Bayelsa, Edo, Bauchi da babban birnin tarayya Abuja.
“Daga cikin Naira biliyan 1.8 gwamnati ta samar da Naira miliyan 600 wanda ma’aikatar kiwon lafiya ta yi amfani da su wajen siyo magungunan, horas da ma’aikata da gina asibitoci.
Ya ce a 2018 gwamnati ta kara samarda Naira biliyan 1.2 da hakan ya sa aka samu daman iya ciyar da yaran dake fama da matsanancin yunwa a jihohi 12 a kasar nan.
“ Da muka gano adadin yawan jihohin dake fama da wannan matsala a kasar nan sai muka aika musu da wasiku domin sanar da su da matsalar dake tunkarar su da kuma irin taimakon da zamu iya yi musu. Sai dai kuma mun yi rashin sa’a domin kuwa da yawa daga cikin jihohi bau ce mana komai ba akai.
Ya roki jihohin da su amsa ma’aikatar sannan su mai da hankali wajen ganin su kawar da matsanancin yunwa ga yara kakana.
Discussion about this post