Sanata Dino Melaye kuma dan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar jam’iyyar PDP ya sha kasa a zaben fidda dan takarar gwamnan jihar Kogi na Jam’iyyar PDP da aka gudanar a Jihar.
Shugaban kwamitin gudanar da zaben kuma Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da ya bayyana sakamakon zaben a Lokoja ya ce Dino ne ya zo na hudu a zaben da kuri’u 70 kacal.
Tsohon gwamnan jihar, Idris Wada shima bai ji da dadi ba domin ko kusa da yin nasara bai yi ba duk da shine ya zo na hudu a zaben da kuri’u 345.
Musa Wada ne ya lashe zaben da kuri’u 748, sannan sai Abubakar Ibrahim da ya zo na biyu da kuri’u 710.
Sauran sun hada da Aminu Abubakar Suleiman, 55; Victor Adoji, 54; Erico Ahmeh, 42; Salihu Atawodi, 11; Mohamed Shaibu, 41 Bayo Averehi, 2; Emmanuel Omebije, 9 da Grace Adejoh, 0.
Sai dai kuma sanata Dino ya ce bai amince da sakamakon zaben ba cewa an yi masa murdiya ne.
Dino ya ce an shigo da sama da kuri’u 600 da basu daga can wani wuri sannan a ka dankarawa Musa Wada da yayi nasara a zaben kuma masu kula da zaben na gani basu ce komai ba.
Yanzu dai za a kara ne tsakanin gwamna Yahaya Bello na APC da Musa Idris na jam’iyyar PDP.
Za a yi zaben gwamnan Kogi ranar 16 ga watan Nuwamba.