Gidauniyar OB Lulu Briggs tare da hadin guiwar asibitin koyarwa na jami’ar jihar Ribas da babban asibiti dake Fatakwal sun yi wa mata 100 fidar cutar kaban ciki a jihar Ribas.
Shugaban gidauniyyar Seyi Lulu Briggs ta bayyana cewa gidauniyyar ta yi haka ne domin tallafa wa mata talakawa dake fama da wannan ciwo.
“Gidauniyyar OB Lulu Briggs gidauniyya ce wanda mijina marigayi Dacta OB Lulu Briggs ya kafa domin tallafa wa mutane musamman talakawan kasarnan.
“Tun bayan rasuwar sa ranar 27 ga watan Disemba, wannan shine karon farko da gidauniyyar ta fara aiki domin talakawa a kasar nan.
Seyi ta ce wannan karon gidauniyar zata yi wa mata dake fama da kaban ciki fida kyauta.
Bayan haka a taron wata likita dake aiki da babban asibiti dake Fatakwal Rosemary Ogu ta bayyana cewa ya kamata a rika yawar wa mutane kai game da wannan cuta.
Ta kara da cewa cutar ya fi kama mata masu shekaru 35 zuwa sama da matan da suka isa haihuwa amma basu haihu ba.
“Sannan koda anyi wa mace fida cutar zai iya dawowa idan har dai mace bata dauki ciki ba bayan shekaru uku da aka yi mata fidar.
Ogu ta ce a takaice dai daukan ciki a lokacin da ya kamata na cikin hanyoyin hana mata kamuwa da kabar ciki.
Discussion about this post