Garkuwa da kashe-kashe sun ragu a fadin Najeriya – Shugaban ‘Yan Sanda

0

Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya, Sufeto Janar Mohammed Adamu, ya bayyana cewa kashe-kashe da sauran ayyukan karya dokokin tsaron kasa ya ragu matuka ainun a Najeriya, a watannin karshen wannan shekara.

Yace haka ta faru ne sakamakon “taron tattauna zaman lafiya da gwamnatin tarayya ta bijiro da shi.”

Ya ce idan aka kwatanta yanzu da kuma can baya, za a fahimci cewa rikice-rikicen tashe-tashen hankila sun ragu sosai.

“Ba mu dade da kammala zaman taron samar da zaman lafiya ba, inda muka fahimci cewa batun tsaro a kasar nan ya na kara inganta sosai.

“ Mun fahimci cewa sata da garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga sun ragu. Haka ma fashi da makami da ayyukan kungiyar asiri.”

Sufeto Janar Adamu ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa, bayan ganawar sa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Daga nan ya kara da cewa tayin afuwar da gwamnati ta yi wa masu garkuwa da mutane ta kara karfafa tsaro a kasar nan.

Gwamnatin Jihar Katsina ta yi zaman sulhu da ‘yan bindiga masu kai hare-hare garuruwa tare da garkuwa da mutane.

Cikin makonni biyu sun damka wa gwamnatin jihar sama da mutane 40 da suka yi garkuwa da su.

A na ta bangaren, gwamnatin jihar Katsina ta saki wasu hatsabiban ‘yan bindiga 9 da ake zargi da kai hare-hare da kuma garkuwa da mutane.

Sufeto Janar Adamu dai ya ce ba da ka ya ke bayani ba. Su na da jadawalin kididdigar da ta nuna raguwar kashe-kashen matuka.

Daga nan ya nuna irin zaman da suka yi da gwamnati da kuma Kungiyar Miyetti Allah, wadda ta nuna musu irin kalubalen da Fulani makiyaya ke fuskanta.

Bayan duba wadannan matsaloli ne aka bada tayin mahara da masu garkuwa da mutane su saki wadanda suka tsare kuma su mika makaman su.

A bangaren wadanda suka ki bada hadin kai kuwa, mun je mun bi mun gano inda sansanonin su suke, musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma hanyar Birnin Gwari, muka ragargaza wadannan sannsanoni na su.

“An kifar da wasu kuma an kama wasu. Shi ya sa a yanzu hare-hare da gwarkuwa damutane suka yi sauki a yankin Arewa maso Yamma.”

Share.

game da Author