HADARIN MINNA: Max Air sun ce an samu matsala a Minna, shugaban hukumar Alhazai Abdullahi ya karyata haka

0

Shugaban hukumar Alhazai na Kasa Abdullahi Mohammed, ya karyata rahoton da aka yada na yadda jirgin Max ya yi saukan gaggawa a filin Minna.

Abdullahi ya ce babu wani abu da ya faru a filin.

” A iya binciken da muka yi ba bu wannan magana wai jirgin Max dauke da Alhazai ya ya yi hadari a filin Minna. Wannan jirgi na Max Air ya sauka lafiya lau sannan ko a sama jirgin bai yi wa matukan gaddama ba. Sun sauka lafiya.

Sai dai kuma maganar Abdullahi ya bambamta da na darektan kamfani Max Air shi kansa, Ibrahim Dill inda ya tabbatar da cewa an samu matsala a lokacin da jirgin ya zo sauka a filin jirgin sama na Minna da Alhazai akalla 550.

Dill ya ce Iska mai karfi da ruwa a sararin samaniya ne ya sa jirgin yin tangal-tangal inda ya nemi ya rika tangal-tangal har Allah ya sa ya sauka a filin jirgin, ” Sai dai kuma daya daga jikin injinan jirgin hudu ya lalace.

Share.

game da Author