DAUKAR ‘YAN SANDA 10,000: Yadda Ministan Shari’a Malami ya yi wa Hukumar Aikin Dan Sanda Kafar-ungulu

0

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasika, inda shawarce shi a kyale Rundunar ’Yan Sanda ta ci gaba da aikin daukar sabbin ‘yan sanda.

Wannan shawara da malami ya bayar kuwa babbar kafar-ungulu ce ya yi wa Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda ta Kasa, wadda a ka’idance ita ce doka ta bai wa damar shirya daukar ‘yan sanda aiki da ma sauran wasu wajiban ayyukan da su ka shafi aikin dan sanda a Najeriya.

Malami ya shaida wa Buhari cewa an dade ba, tun yau ba ake ‘yar-tsama da rashin jituwa tsakanin Rundunar ‘Yan Sanda da kuma Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda.

Amma dai a wannan karon, a bar ‘yan sandan su dauki sabbin jami’an su da kan su, ba ita Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda din ba. Haka PREMIUM TIMES ta tabbatar Malami ya rubuta a cikin wata wasika da ya aika Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Baya ga wannan, Malami ya nemi a gaggauta yi wa Dokar ’Yan Sanda ta Police Act, da ta Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda Kwaskwarima.

Yin haka a cewar Malami zai rage ko ya magance abin kunyar sabanin da ke faruwa a tsakanin hukumomin biyu.

A karshen wannan shekara ne dai za a fara daukar sabbin ‘yan sanda, wato na 2020 kenan.

An samu sabani tsakanin Rundunar ’Yan Sanda da kuma Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda a kan wanda ke da ikon daukar kuratan ‘yan sanda 10,000 a wannan shekarar.

Rikicin ya yi tsamari tun cikin makonni hudu da suka gabata, inda hukumar ta zargi Sufeto Janar Muhammad Adamu da yi wa jerin sunayen wadanda za a dauka aikin dan sanda ‘yar asarkala.

An zargi Sufeto Janar Adamu da baddala wasu sunayen.

Sai dai kuma Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa ta karyata wannan zargi cewa maras tushe ne, babu gaskiya, kirkira ce kuma sharri ne kawai.

Daga nan sai ta shawarci Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda da ta tsaya matsayin da aka ajiye ta.

Hedikwatar ta ce Rundunar ‘Yan sanda na da ikon duba sunayen wadanda za a dauka aikin kurtun dan sanda a kasar nan.

Tuni dai Rundunar ‘yan sanda ta karbi fam na matasa 315,032 masu neman aikin kurtun dan sanda. Kuma 10,000 kacal za a dauka. Tun a ranar 11 Ga Janairu, 2019 aka rufe cika fam.

Sabanin da ya faru tsakanin Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda da kuma Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda, ya sa Hukumar ta dakatar da shirin daukar kuratan ‘yan sandan aiki su 10,000, tun a cikin watan Agusta.

Hukumar ta bayyana cewa ita ce doka ta bai wa ikon yi wa ‘yan sanda karin girma, dakatarwa, kora, hukuntawa ko yi musu canjin wurin aiki.

Sai dai kuma wannan umarni ya bi ta bayan kunnen Sufeto Janar Adamu, domin baya ga bijirewa, Adamu ya kuma bada umarni a fadin kasar nan cewa a ci gaba da aikin tantance kuratan da za a dauka, ta hanyar binciken lafiyar su da sauran binciken tantancewar da duk suka wajaba a yi musu.

Adamu ya ce Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda ba ta da ikon tsoma baki wajen daukar kuratan ‘yan sanda.

Tsoma bakin da Malami ya yi a wannan tirja-tirja a ranar 16 Ga Satumba, ta fito fili ne a cikin wasikar da ya rubuta wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.

PREMIUM TIMES ta samu kwafen wannan wasika, wadda Malami ya ce a kyale Sufeto Janar Muhammad Adamu ne ya kamata ya ci gaba da aikin daukar kuratan ‘yan sandan 10,000.

Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai san da batun wasikar da Malami ya aika Fadar Shugaban Kasa ba.

Share.

game da Author