Attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, kuma bakar fatar da ya fi saukan bakaken fatar duniya arziki, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya na fatan ganin zuwan ranar da shi ma zai sadaukar da rabin dukiyar sa wajen ayyukan jinkai, musamman bangaren inganta kiwon lafiya.
Dangote ya yi wannan bayani jiya Laraba, inda ya nuna muradin ganin shi ma “ya bi irin sahun da Bill da Melinda Gates su ka bi, wajen gudanar da ayyukan jinkai da dukiyar su.”
Shi ma Dangote ya kafa ta sa Gidauniyar Dangote a nan Najeriya, tun cikin 1994. Ya ce bai san irin gagarimar gudummawar neman agajin da ake matukar bukata a Najeriya ba, sai da ya hadu da Bill Gates.
Dangote na daya daga cikin attajirai da mashahuran mutanen da aka gayyata New York wurin taron Majalisar Dinkin Duniya na 74.
Daga nan sai ya yi magana a kan matsalar abinci mai gina jiki a Afrika, musamman ga kananan yara, inda ya fi maida hankali a kan buga misali da Najeriya, inda shi da Bill Gates su ka fi maida hankali wajen gudanar da ayyukan jinkai a bangaren inganta kiwon lafiya.
Ya ce haduwar da ya yi da Bill Gates ta canza masa alkibla sosai, ta yadda ya kara ganin martaba da kima da darajar dan adam da ayyukan jinkan al’umma.
Ya ce bai san akwai gagarimin kalubalen bukatar jinkai cikin al’umma ba, har sai da Gidauniyar sa ta hada hannu da Gidauniyar Bill da Melinda.
Daga nan ya nuna rashin damuwa da matsalar abinci mai gina jiki a wajen kananan yara a Najeriya. Ya ce akwai bukatar a shawo kan wannan babbar matsala.
Dangote ya kara da cewa su na tattaunawa da gwamnatoci a Najeriya ta yadda za a fito da tsarin da zai inganta da habbaka masana’antun abincin zamani, musamman domin watada abinci masu gina jiki don kananan yara.
Ya ce za a iya cimma wannan kudiri ta hanyar inganta dukkan abincin yara da sinadirai masu gina jiki.
“Ba mu da wani abincin da ya wuce shinkafa a Najeriya. Ita suke ci da safe, da rana da kuma dare. A yanzu haka kamfanin Dangote na kan hanyar rika samar da shinkafa wadda za a rika sirka wa sinadaran gina jiki a ciki. Kuma za mu rika samar da sama da tan daya.”