Gwamnatin jihar Filato da hadin guiwar (UNICEF) sun kebe ranaku biyar domin wayar da kan mutane da yi wa mata da mata masu ciki allurar rigakafin dafin tsatsa a jihar.
Jami’ar wayar da kan mutane na hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta jihar Jerisha Kakwi ta fadi haka a taron wayar da kan masu ruwa da tsaki game da kau da matsalar dafin tsatsa da aka yi a garin Jos ranar Talata.
Kakwi ta ce za a fara wayar musu da kai ne da fara yi musu allurar rigakafin daga ranar 27 ga watan Satumba zuwa ranar daya ga watan Oktoba a kananan hukumomi 16 daga cikin 17 din dake jihar.
Ta ce za a yi wa mata da mata masu ciki da masu shayarwa dake da shekaru 15 zuwa 49 allurar rigakafin a wannan lokaci.
Kakwi ta ce gwamnati za ta yi haka ne domin kare rayukan mata da jarirai daga kamuwa da wannan cutar.
Dafin tsatsa wato ‘Tetanus’ abu ne dake yawan kama mata da jarirai da ya kan sa ba za a iya motsa jiki ba idan ya kama mutum matuka.
Kwayoyin cutar kan shiga jikin mutum idan mutum na da rauni a sannan jaririn dake cikin uwarsa kuwa zai kama cutar ta jinin mahaifiyarsa.
Alamun cutar sun hada da zazzabi, rashin iya motsa jiki da sauran su.
Kakwi ta yi kira ga mata musamman masu ciki da su rika zuwa asibiti domin yin awon ciki, yin allurar rigakafin cutar sannan su guji haihuwa a gida domin haihuwa a gida na dag cikin hanyoyin dake haddasa cutar a jarirai.
Sannan ta karyata camfe-camfen da ake yi wai duk wanda ya kamu da cutar maye ne.