CHAMPIONS LEAGUE: Wa zai lashe kofi, wa zai lashe baki?

0

A duk shakarar da kakar wasan Zakarun Turai na Champions League ya zo, zaka ji magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa na cewa Barcelona ce za ta dauka. A’a, Real Madrid dai ko kuma Bayern Munich. Daga baya bayan nan kuma an rika kara Juventus, Liverpool, PSG da sauran su. Kafin nan ana karawa da irin su Chelsea da Manchester United har Atletico Madrid.

Kafin gasar 2018/2019, a cikin shakaru 10 da suka gabata, Madrid, Barcelona da Bayern sun lashe kashi 80 bisa 100 na Kofukan Zakarun Turai. Barca ta ci uku, Bayern sau daya yayin da Madrid sau hudu.

Sai dai kuma wannan duk ya canja shekarar da ta gabata, yayin da Liverpool ta lashe kofin.

Karfin Liverpool ya dawo tun shekaru biyu da suka gabata, inda a 2017/2018 ta buga wasan karshe tare da Real Madrid, yayin da ta lashe kofin a shekarar da ta gabata, 2018/2019.

Bayan su akwai wasu kungiyoyin da suka kawo karfi, irin su Manchester City, wadda ta yi kaka-gida a wasan Premier na Ingala, kuma ta zamae wa sauran kungiyoyi irin su Manchester United, Chelsea da Arsenal gagarabadau.

Har yanzu dai fitattun ‘yan wasan da suka mamaye duniya wato Leonel Messi da Cristiano Ronaldo na nan da karfin su. To a ina ake tunanin kofin zai fada? Wa zai lashe kofi, wa zai lashe baki?

Kungiyoyi da dama sun zuba kudade sun sayi sabbin ‘yan wasa, musamman ganin cewa kama daga Premier League zuwa La Liga, babu kungiyar da ta samu maki 100, hatta wadanda suka zo na daya.

Idan Giardiola zai iya yin irin kokarin da ya rika yi Barcelona, to wannan shakarar Manchester City za ta ita sa ran daukar kofi.

Barcelona za ta iya sa ran daukar kofi, matsawar za ta farka daga barcinn irin yadda ake yi mata sakiyar da babu ruwa. Shekaru biyu da suka gabata, sun ci Roma kwallaye uku. Amma sai da Roma ta rama, har ta kara musu, ta fitar da su.

Haka a shekarar da ta gabata sun ci Liverpool kwallaye uku, amma sai da Liverpool ta rama kwallayen ta, har ta kara mata daya, aka tashi 4:0. Wane irin sakaci ne wannan? Me ke janyo musu irin wannan wala-walar?

Da dama na ganin cewa karfin Barcelona dai na Messi ne. Amma kuma duk da shi aka buga wasannin da Roma da Liverpool suka kunyata Barcelona a shekaru biyu da kuma shekarar da ta gabata. Ga shi kuma shekarun sa sun fara ja, ya haura 30.

Liverpool a yanzu ita ke jan ragamar ta daya a gasar Premier. Har ma ta tsere wa Manchester City da maki biyar. Duk da dai yanzu aka fara gasar, ba a yi nisa ba.

Hatsabiban ‘yan wasan ta uku, Mohamed Salah, Roberto Firmino da Sadio Mane na nan daram su na damawa su shanye yadda suke so a cikin fili.

Har yanzu da sauran gyara a Juventus, duk kuwa da cewa Ronaldo na faffakar sa sosai a kungiyar. Da alama wannan shekarar za su tabuka abin kirki, amma fa da wahalar gaske su ji kamshin kofi.

Rabon da Pep Guardiola ya ci kofin Champions League tun 2010/2011. Ko zai iya kai gaci a wannan gasa ta 2019/2020.

Real Madrid sun lashe 2015/2016 sai 2016/2017 da kuma 2017/2018 duk a jere. Amma ba su yi nisa a 2018/2019 ba.

Babbar takamar da Madrid ke yi ita ce, ba su taba zuwa wasan karshe aka doke ta ba, sai ta kai ga kofi. Shin za su iya kaiwa ga wasan karshe a wannan kakar gasa?

To abin tambayar a nan, ko sun yi shirin daukar wannan kofi a wannan shekarar ko wannan kakar kuwa? Da wahalar gaske.

Bari mu ga ko PSG, Atletico Madrid da sauran wasu kungiyoyin da ake kallon cewa ‘yan rakiya ne ko za su iya tabuka wani abu?

Ba za mu manta da rawar da Ajax ta taka a shekarar da ta gabata ba, inda ta kori Real Madrid da Juventus. Sai dai kuma za mu zura ido mu ga a wannan kakar, za ta buge maza ta ci kofi, ko kuwa sammakon-bubukuwa za ta yi?

Share.

game da Author