CHAMPIONS LEAGUE: Ko PSG za ta iya yi wa Madrid jina-jina?

0

Jiya Talata ne aka fara fafatawa, gurugubji, karimtsa da rimatson gasar neman cin Kofin Zakarun Turai na kakar 2019/2020.

An saba fara wasan tsakanin 10 zuwa 11 Ga Satumba, amma wannan karon sai 17 Ga Satumba za a fara.

Kungiyoyi 24 za su fafata, inda a yau Talata 12 za su fafata, haka gobe Laraba ma wasu 12 su sake fafatawa, duk a wannan zagaye na farko.

Wasan da zai fi daukar hankali shi ne wanda za a buga tsakanin PSG da Real Madrid. Za a buga wasan a birnin Paris na kasar Faransa.

Sai dai kuma Madrid za ta buga wasan ba tare da wasu kwararrun ‘yan wasan ta da suka ji ciwo ba.

Goal.com ta ruwaito cewa cikin wadanda ba ba za su buga wasan ba, akwai Marcelo wanda ya ji ciwo a wuyan sa a wasan La Liga da Madrid ta ci Levente 3:2. Sai Isco, Modric da Marco Asencio.

Haka kuma kaftin na Madrid Sergio Ramos da Nacho duk ba za su buga wannan wasan farko ba, saboda su na da katin gargadi tun a wasan 2018/2019, a ranar da Ajax ta fitar da su. Katin gargadin su ya nuna ba za su buga wasa na gaba ba. Wannan wasan kenan.

Yayin da Madrid ta bayyana cewa sabon dan wasan ta Hazard zai fara buga wasan tun tashin farko ba a kan benci za a ajiye shi ba, za a sha kallon ko Neymar da Mbappe za su iya yin wasan kura da yaran Zidane.

‘Yan Wasa 19 da za su buga wa Madrid wasa da PSG

Masu Tsaron Gida: Courtois, Areola and Altube.

Masu Tsaron Baya: Carvajal, Militão, Varane, Odriozola, Mendy and De la Fuente.

’Yan Tsakiya: Kroos, Casemiro and James.

’Yan Gaba: Hazard, Benzema, Bale, Lucas V, Jović, Vinicius Jr. and Rodrygo.

SAURAN WASANNIN YAU LARABA

Olympiacos vs Tottenham

PSG vs Real Madrid

Atletico Madrid vs Juventus

Shakhtar vs Manchester City

Beyern Munich vs Red Star Belgrade

Dinamo Zagreb vs Atalanta

Share.

game da Author