Buhari ya sauya wa ministoci biyu ma’aikatu

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari amince da sauya wa wasu ministocin sa biyu ma’aikatu.

Wadanda aka canja wa ofisoshin sune Karamin ministan Neja Delta, Festus Keyamo, an mai da shi karamin ministan Kwadago.

Shi kuma Senator Tayo Alasoadura zai maye gurbin Keyamo a ma’aikatar Neja Delta.

Darektan yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya sanar da haka ranar Talata.

Share.

game da Author