Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Kori shugabar ma’aikatan gwamnati, Winifred Ekanem Oyo-Ita sannan ya sanar da nada Mrs. Folashade Yemi-Esan a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin Tarayya.
A takardar da Darektan yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar, Oyo-Ita za ata ba da wuri ne domin ba hukumar EFCC daman bincikar ta kamar yadda ta fara.
Baya ga haka Buhari ya kara wa wasu manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin tarayya wa’adin shekara daya, bayan wa’adin aikin su ya kara.
Babban dalilin yin haka kuwa a cewar shugaba Buhari, shine domin a samu a kammala shirya kasafin kudi na 2020, sannan kuna su nuna wa sabbin da za a nada nan da watanni 12 inda aka tsaya da inda za a tashi.
Ga sunayen wadanda aka kara wa wa’adin aiki
1 – Mrs. Georgina Ehuriah – Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida
2 – Mrs. Ifeoma I. Anagbogu – Ma’aikatan Harkokin Mata
3 – Mrs. Grace Gekpe – Ma’aikatar Yada Labarai
4 – Dr. Umar M. Bello – Ma’aikatar Ayyukan Gona da Da Raya Karkara
5 – Suleiman Mustapha Lawal – Ma’aikatan Harkokin Kasasshen Waje
6 – Mrs. Comfort C. Ekaro – Ma’aikatan Albarkatun Ruwa
7 – Mr. Olusegun A. Adekunle – Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya