Budurwa ta kashe saurayin ta don ya ki bata kudin kitso

0

A wani fadan masoya da ya auku a garin Ado Ekiti jihar Ekiti, wata budurawa mai suna Bukola Odeyemi ta kashe saurayinta John Iju a dalilin kin bata kudi taje ta yi kitso.

Shekarun Bukola 20 shi kuma Iju shekarun sa 22 sannan duk suna karatun su ne a jami’ar jihar Ekiti.

Sai dai kuma a daren Talata wato shekaran jiya ke nan Bukola ta je gidan Iju inda ta bukaci ya bata kudin kitso har Naira 2,500.

Shi kuwa Iju yace mata bashi da kudin da zai iya bata domin yin kitso a wannan lokaci.

Wannan bayani da yayi bai gamsar da ita ba sai suka fara dan cacan baki a kai.

Da abin ya bata masa rai, saurayin sai ya lakadawa Bukola dukan tsiya inda a dalilin haka kuwa ta dauki wani wuka dake ajiye a tire ta caka masa a kirji.

Nan take Iju ya yanke jiki ya fadi daga nan sai ya ce ga garin ku nan.

Makwabta da abokan Iju ne suka kai karan aikata wannan ta’asa da Bukola ta yi a ofishin ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Caleb Ikechukwu ya bayyana cewa Bukola na nan tsare a hedikwatar ‘Yan sanda sannan da zaran sun kammala bincike za a mika ta kotu domin yanke mata hukunci akan abin da ta aikata.

Share.

game da Author