Akalla sojoji 13 aka kashe a wasu hare-hare na kwanan nan, da ke nuna cewa Boko Haram sun sake yunkurowa da karfin tuwo.
A wadannan hare-hare, an tabbatar da cewa baya ga kisan sojojin 13, sun kuma arce da dimbin manyan kayan yaki wadanda suka kwata daga hannun sojojin.
Sai dai kuma har yau ba a ji komai ba daga bakin hukumar tsaro ta soja dangane da hare-haren wadanda suka fara kai wa sojojin tun ranar Lahadi da ta gabata.
A ranar Juma’a manema labarai sun ritsa Kakakin Hukumar Jojojin Najeriya, Sagir Musa domin a ji ta bakin sa, amma ya ki amsa musu tambaya dangane da wannan gumurzu.
Amma wata majiya a cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa: “A gaskiya wannan mako da ya shige, sojoji ba su wanke sun sha da dadi ba. Sai dai kuma majiyar ta roki a sakaya sunan ta, don kada cibi ya zama kari.
“Sojojin da ke sintiri kusa da Gajigana sun afka cikin kwanton baunar Boko Haram. Kuma sun kashe da yawa.” Inji majiyar.
Sannan kuma a ya kara da cewa Boko Haram cike da Manyan motocin yaki sun kai wa Sojojin Musamman da ke Gudumbali hari.
An kai wannan hari ne inji majiyar mu a kan hanyar Gurunda zuwa Zari.
Majiyar ta kara da cewa sojoji kusan 100 da suka tsere daga harin na Boko Haram sun sheka har zuwa garin Damasak, garin da ke kan iyakar Najeriya da Nijar, bayan bayan kwanaki.
“A yayin da na ke maka magana din nan, an kashe sojoji bakwai, kuma akwai yiwuwar an kara kashe wadansu ma. Saboda an ce Boko Haram sun rika yi wa wadanda suka kama yankan rago. Kuma sun daure su da igiya a jikin motoci, suka rika jan su kasa.”
Majiyar ta ce a ranar Laraba da ta gabata ce aka kwashi gawarwakin zuwa hedikwatar Rundunar Soja ta 7 da ke Maiduguri.
Sannan kuma Boko Haram sun sake kai wani harin a Kukawa, a ranar Laraba, lokacin da sojojin Runduna ta 7 ke tsakiyar jimami da alhinin kisan wadancan sojojin da aka kai musu gawarwakin su.
Duk da an ce ba a samu rahoton kisan soja ko daya ba a Kukawa, “amma dai maharan sun kwashi manyan makamai sun yi gaba da su.”
Sannan kuma an sake kai hari a Gubio a ranar Alhamis. Dama kuma makonni uku da suka gabata an kai hari a can.
An kai wa Gubio hari a daidai lokaci daya da Gajiram da kuma Gajiganna.
Majiya ta ce an kashe sojoji shida tare da dauke bindigogi uku da Toyota Hilux ta CJTF a harin Gubio.”
An fi sanin dan CJTF din da aka kashe a Gubio Bulama Bukar da suna ‘Maradona’. Dama kuma Boko Haram sun dade da shan alwashin sai sun kashe shi. Saboda Kwamanda ne sukutum.
Da aka tambayi Sagir Musa, sai ya ce a tambayi Kwamandan Tsara Yaki a Maiduguri.
Babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai, ya ce Maiduguri a cikin makon, amma bai yi magana a kan wannan barna da aka yi wa sojoji ba.