An tabbatar da cewa Boko Haram sun kashe daya daga cikin ma’aikatan agaji na kungiyar Action Against Hunger shida da suka yi garkuwa da su.
’Yan ta’addar ne da kan su suka tura bidiyon da ke nuna yadda suka fille masa kai a soshiyal midiya.
Dan jaridar nan Ahmed Salkida ya sanar da wannan mummunan labari ta shafin san a Twitter, inda aka nuna wani hoto dishi-dishi mai nuna yadda wani mutum mai rufe da fuska ya sare kan daya daga cikin wadanda su ke garkuwar da su.
Hedikwatar kungiyar ceto da agaji ta Action Against Hunger da ke Faransa, ta tabbatar da kisan daya daga cikin ma’aikatan na ta ga PREMIUM TIMES.
Idan ba a manta ba, a ranar 18 Ga Satumba ne sojoji suka tilasta wa kungiyar agajin ta AAH ta rufe ofishin ta da ayyukan da ta ke yi, bisa zargin wai ta na taimaka wa Boko Haram.
Sanarwar da Salkida ya fitar a shafin sa na Twitter, ya ce :#ISWAP sun kashe daya daga cikin ma’aikatan Action Against Hunger su shida da suka yi garkuwa da su watanni biyu da suka gabata a Barno.”
Sanarwar ta tabbatar da cewa wanda aka kashe din namiji ne.
Kungiyar Boko Haram sun ce sun kashe shi ne saboda sun lura gwamnati yaudarar su kawai ta ke yi, dangane da tsawon lokacin da aka dauka ana tattaunawa a asirce da masu shiga tsakanin su.
“ISWAP sun kuma yi barazanar kashe sauran ma’aikatan biyar da har yanzu ke tsare a hannun su.”
Discussion about this post