Gwamnonin Najeriya sun afka cikin jula-jular tunani da fargabar umarnin da Gwamnatin Tarayya ta fito ta fito da shi, cewa za a fara cire kudaden ramcen da aka ba su a tsakanin 2015 zuwa 2017.
Gwamnatin Tarayya ta rika gabzar lamunin kudade ta na ba su daga cikin kudaden Faris Club domin toshe kofofin fatara da karancin nauyin aljifai da suka shiga a lokacin, inda har biyan albashi ma ya rika gagarar su.
Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta kididdige jimillar kudaden da gwamnatin tarayya ta narka wa jihohi cewa sun kai adadin naira bilyan 614.
An rika bai wa jihohi kudaden ne a matsayin wani zanin rufe katara tsakar kasuwa, a lokacin da babu riga ko fatari.
Sunan tsarin wanda gwamnati ta shigo da shi a lokacin, wato National Bugdet Support Loan Facility. Ma’ana, Kudaden Lamuni Domin Tallafawa Kasafin Kudi.
Yayin da ta ke bayani dangane sabon tsarin yadda jihohi za su biya bashi, Minstar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, ta ce kowace jiha za ta biya naira bilyan 17.5
Tuni dai har gwamnatin tarayya ta tsara yadda za a fara karbar kudaden, inda za ta kafa kwamitin da ya kunshi wasu daga cikin gwamnaoni da jami’an Babban Bankin Najeriya da kuma jami’ai daga Ma’aikatar Harkokin Kudade ta Kasa.
Jihohi dai sun fara karbar wannan lamuni daga gwamnatin tarayya tun bayan da matsin tattali ya kai su ga kasa biyan albashi da sauran gudanar da ayyukan gwamnati ko gyare-gayaren kayayyayin more rayuwar al’umma da suka lalace, tum a cikin 2016.
Dama kuma gwamnatin tarayya ta rika bayar da lamunin ne a bisa sharadin cewa kowace jiha ta tabbatar ta biya albashin ma’aikata da kudaden.
Binciken PREMIUM TIMES ya gano cewa, tun bayan da Ministar Harkokin Kudade ta fitar da sanarwar shirin fara neman a gwamnoni su biya bashi, sun shiga tsugune-tashi da fagamniyar yadda kauce, ko waskewa ko kuma baude wa biyan bashin.
Duk wani kokari da PREMIUM TIMES ta yi domin jin ta bakin ko da gwamna daya ko kwamishinonin jihohi na harkokin kudade, ya ci tura. Babu gwamna ko kwamishinan da ya yarda ya yi magana.
Sai dai kakakin yada labarai na wani gwamnan Kudu maso Yamma, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu gwamnan da zai yarda ya yi magana shi kadai.
Amma dai ya ce gwamnonin za su taru su amince da daya daga cikin su zai yi magana da ‘yan jarida, a madadin Kungiyar Gwamnonin Najeriya.
Wannan kakakin yada labarai shi ma ya nemi a sakaya sunan sa da sunan gwamnan da ya ke wa aiki.
“Ina tabbatar maka babu wani gwamnan da zai iya yi maka magana a kan wannan batun a yanzu. Saboda kowane cikin sa ya duri ruwa. Ka kuma san irin halin rashin kudin da ya ke addabar jihohi.
“Tabbas na san za su fitar da matsayar su, musamman na san yanzu su na ta kokarin taron neman mafita tsakanin su da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.”
Wani makusancin Shugaban Kungiyar Gwamninin Najeriya, Kayode Fayemi, ya shaida wa wakilinmu cewa: “Gwamnoni da yawa na cikin fargaba, musamman saboda yawancin su sabbin-yanka-rake ne, ba ma su suka karbi lamunin daga daga gwamnatin tarayya ba.
“Ya za ka ji idan aka zabe ka cikin watan Mayu, sannan a cikin watan Agusta a ce maka ka fara biyan bashin da ba kai ne ka ciwo shi ba?”