BAYA TA HAIHU: Kashi 7.5 ne karin Harajin ‘VAT’, ba 7.2 ba – Gwamnati

0

Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, ta yi karin hasken cewa daga kashi 5℅ bisa 100℅ zuwa 7.5% aka kara kudin Harajin Kayayyaki, ba zuwa kashi 7.2% ba.

Zainab ta ce amma ba yanzu za a fara aiki da sabon tsarin biyan harajin ba tukunna, har sai Majalisar Tarayya ta amince, kuma ta yi wa Dokar Harajin ‘VAT’ kwaskwarima.

Kakakin Yada Labarai na Minista Zainab, mai suna Yunus Abdullahi ne ya yi wannan karin haske a jiya Juma’a, inda ya kara cewa an bijiro da wannan karin ne biyo bayan shawarwarin da Majalisar Bada Shawara Kan Tattalin Arziki ta nemi a yi wannan karin a matsayin hanya daya tilo da za a bi domin a iya biyan kudin karin mafi kankantar albashi.

Yunus ya ce wannan kwamiti da ke karkashin kwararraren masanin tattalin arziki mai suna Bismack Rewane, an kafa shi ne tun a ranar 9 Ga Janairu. Ya ce kwamitin ya kunshi kwararrun masana tattalin arziki daga bangaren gwamnati da kuma masu zaman kan su.

Yunus ya ce kwamitin ya mika rahoton sa tun a ranar 21 Ga Maris, inda ya kawo hujjar a yi karin harajin kayayyaki daga 5% zuwa 7.5%. Ya ce hakan zai samar da kudaden da za a iya kara samu ana bai wa tarayya da kuma musamman jihohi da kananan hukumomi domin su samu su iya biyan karin albashi.

Wannan kwamiti ya nuna cewa ai wannan kari ba zai jigata aljifan ‘yan Najeriya ba, idan aka yi la’akari da cewa yawancin kasashen Afrika da duniya ma harajin su na ‘VAT’ ya nunka na na wanda ‘yan Najeriya ke biya.

Kwamiti ya kara wa gwamnati kwarin gwiwar karin kudin harajin kayayyakin tare da nuna mata cewa jihohi da kananan hukumomi za su ci moriya sa sosai, domin su ne za a rika dumbuza wa kashi 85 bisa 100 na kudaden idan an tara su.

Sannan kuma gwamnati ta gamsu da hujjar da kwamitin ya bayar cewa yin karin harajin zai samar da makudan kudaden da za a magance ko ya rage yawan ciwo bashi da gwamnatoci ke yi domin biyan albashi. Kuma zai cike gibin kudaden da ake samu a kasafin kudi, musamman a kudaden ayyukan yau da kullum.

Sai dai kuma ya ce kafin a fara amfani da wannan sabon tsarin haraji, sai Majalisar Tarayya ta yi sa Dokar Harajin ‘VAT’ kwaskwarima tukunna.

Daga nan kuma minista ta lissafa kayayyakin da wannan karin haraji ba su shafa ba. Kuma ta ce wannan kari zai sa su kan su kananan hukumomi samun kudaden da za su maida hankali wajen inganta kiwon lafiya, ilmi da sauran fannonin kyautata rayuwar al’ummar karkara.

Idan ba a mata ba, bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da karin albashi.

PREMIUM TIMES ta buga labarin inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su fito da hanyoyin da gwamnati za ta rika samun kudaden da za ta biya karin albashi da su, ba tare da ta ciwo bashi ba.

Share.

game da Author