BASHIN BILYAN 614: A fara biyan mu bashin da mu ke bin Gwamnatin Tarayya –Inji Gwamnoni

0

Gwamnonin Najeriya sun bayyana wa gwamnatin tarayya cewa batun bashin da aka ce sai sun biya daga watan Agusta din nan, na naira bilyan 614, za su biya, amma ta wata siga daban, ba wai a rika kamfatar kudin su ba.

Gwamnonin sun bayyana wa Gwamnatin Tarayya cewa ai su ma su na bin ta dimbin bashi na aikin gyaran titinan gwamnatin tarayya da suka rika yi, wadanda gwamnatin tarayya din ta ki gyarawa, amma su kuma su ka gyara.

Gwamnonin Jihohi kan gyara titinan gwamnatin tarayya bisa sharadin cewa za a biya su kudin aikin da suka yi, a titinan da gwamnatin tarayya din ba ta maida hankalin gyarawa ba.

Gwamnoni sun yanka wannan sharadin ne a taron su da suka gudanar na Kungiyar Gwamnonin Najeriya, jiya Laraba a Abuja.

Idan ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta rika bai wa jihohi 35 wadannan kudaden ceto su daga kuncin fatarar kasa biyan albashi, tun daga cikin 2017.

An rika ba su kudaden kai-tsaye daga Babban Bankin Najeriya (CBN) daga cikin kudaden Paris Club, da sunan lamuni.

Sun rika biyan albashi da kudaden fanshon ma’aikata da kudaden, a bisa sharadin cewa kowace jiha za ta biyan kudin bayan shekaru biyu, tare da kara kudin ruwa na kashi 9 bisa 100 na kudin da kowace jihar ta karba daga gwamnatin tarayya.

Cikin makon da ya gabata ne wa’adin biyan bashin ya cika, inda nan take gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara wazge kudaden ta daga asusun gwamnonin daga karshen watan Satumba da mu ke ciki.

PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo cikakken labarin wannan katankatana a farkon makon da ya gabata.

Bayan tashi taron da Gwamnonin Najeriya suka yi jiya Laraba a Abuja, Shugaban Kungiyar Gwamnoni na Najeriya, Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, ya bayyana cewa gwamnonin za su biya bashin, amma sai an biya su bashin kudin gyaran titinan gwamnatin tarayya da su ma suka yi, wanda wannan aikin alhalin gwamnatin tarayya ne, kuma har yanzu ba a biya su ba.

“Magana a nan ita ce, idan ka ramci kudi, to ka biya. Gwamnoni kuwa ba su taba nuna kyashi ko jikarar biyan irin wannan lamuni ba, wanda aka karba a bisa sharudda na doka. Amma kuma ba mu so a shiga halin da tsarin kudaden mu zai shiga jula-jula.

“Amma kuma yayin da mu ke kokarin biya, to mu ma fa mu na so a tabbatar mana da saisaita mana bashin da muke bin gwamnatin tarayya, wanda muka rika yin ayyukan da suka wajaba ita ce ta yi, bisa sharadin daga baya za a biya mu. Wannan shi ne batun da mu ke cike.” Inji Fayemi.

Idan ba a manta ba, a wurin wani taro a makon da ya gabata ne Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta bayyana cewa za a fara cire kudaden da ake bin jihohi 35 bashi, daga cikin kudaden kasafin karshen wata da Gwamnatin Tarayya ke ba su na karshen watan Satumba.

Ta ce za a yi amfani da kudaden wajen kara wa daben kasafin kudi na 2020 karfi da kuma makuba.

Share.

game da Author