BARNO: Matsalar yunwa ta ki ci, ta ki cinyewa – Ma’aikatan lafiya

0

Ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Barno ta bayyana cewa matsalar yunwa musamman a yara kanana ta ki ci ta ki cinyewa a jihar.

Ma’aikatar ta kara ce duk da yawan tallafin da jihar ke samu daga gwamnati da kungiyoyin bada agaji, har yanzu jihar na fama da wannan matsala na matsanancin yunwa musamman ga yara kanana.

A 2016 kungiyoyin bada tallafi da gwamnatin jihar Barno sun tallafa wa yara kanana 500 a karamar hukumar Bama da ke fama da matsanancin yunwa.

Sannan a tsakanin watannin Oktoba 2016 zuwa Mayu 2019 asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya ta rika ciyar da yara kanana 233,000 dake fama da yunwa a jihar.

Daga nan ma kungiyar DFID ta bada gudunmawar dala miliyan 10 domin kawar da wannan matsala amma har yanzu ana nan jiya iyau.

Yakaka Babagana dake aiki a asibitin Muna, dake cikin sansanin ‘yan gudun hijira a jihar ta bayyana cewa matsalar yunwa da yara kanana ke fama da shi na matukar tayar musu da hankali domin a duk rana sai an kawo akalla yara bakwai zuwa goma dake fama da matsanancin yunwa da har sai an duba su an kuma tallafa musa da abinci da magunguna.

Zainab Ali-Goni ma’aikaciyar daya daga cikin asibitin Muna ne. Ta ce a duk sati asibitin kan samu yara 30 zuwa 40 da suke bukatan kula saboda fama da yunwa.

Ta ce hakan na da nasaba ne da yawan-yawan hare-haren Boko Haram da har yanzu wasu bangarorin jihar ke fama da shi.

Manajan sashen kawar da yunwa na asusun UNICEF Sanjay Das ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram ne babban matsalar dake hana su samun nasarar ayyukan kawar da yunwa a jihar.

Das yace sauran matsalolin sun hada da ambaliyar ruwa, nisan asibiti daga kauyuka musamman a yankin kudancin jihar, rashin tsaftace muhalli da jiki, rashin cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki da rashin isassun asibitoci.

Ya ce duk da haka UNICEF ta karo musu tallafin Naira biliyan 9.8 da a yanzu haka suke amfani da su domin aiwatar da sabon shirin kawar da yunwa a jikin yara kanana a jihar.

Das ya ce sabon shirin ya kunshi samar da isassun magungunan kawar da yunwa a jikin yara sannan da wayar da kan iyaye kan hanyoyin gujewa da zasu rika bi domin ceto ‘yayan su daka fadawa matsalar matsanancin yunwa.

Ya ce shirin ya fara aiki tun a watan Afrilun 2019 sannan zai ci gaba har zuwa watan Maris 2022.

“Wannan karo burin mu shine kawar da yunwa a jikin yara sama da 87,000 wadanda suke a tsakanin shekaru uku a jihar.

Share.

game da Author