Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya ba za ta ka jefa ‘yan Najeriya cikin halin kunci da talaucin da su ke fama da shi ba.
Maimakon haka inji Buhari, Gwamnati za ta ci gaba da laluben hanyoyin da za ta rage da mabance wa jama’a radadin kunci da wahalhalun da su ke fama da su.
A kan karin kudin fetur
“A kan karin kudin fetur, na yarda da ku cewa akwai bukatar a kakkabe cin hanci da rashawa da kuma harkallar da ta dabaibaye fannin harkokin mai. To ina tabbatar muku da cewa wannan gwamnati ba ta da wata niyya ko fatan kara wa jama’a kunci da wahalhalu fiye da wadanda suke fama da su.”
Haka Buhari ya bayyana wa sabbin Shugabannin Haddiyar Kungiyoyin Kwadago (TUC, a karkashin shugaban su Quadri Olaleye, a Fadar Gwamnati, Abuja.
Buhari ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya na kan bakan ta na kari mafi kankantar albashi, tare da nuni da cewa taron Majalisar Zartaswar da aka gudanar jiya Laraba sai da ya tattauna tsare-tsaren da za a bijiro da zu na kusa da na nesa, wanda ya hada da batun karin albashi.
Buhari ya ci gaba da bayyana wasu nasarori da gwamnatin sa ta samar a farkon zangon mulkin sa, tare da yin magori wasa kan ka da kan ka.
An kusa fara jin dadin wannan gwamnati
“Duk da cewa ayyukan da muka gudanar sun fitar da Najeriya daga cikin halin matsin tattalin arziki, har yanzu ba a kai ga ji ko ganin alfanun su ko cin moriyar su ba tukunna.
“Amma dai nan da shekaru hudu masu zuwa dai kam za mu ci gaba da irin wannan kokari. Kuma da yardar Allah za mu fitar da milyoyin ‘yan Najeriya daga cikin kunci, fatara da talauci.”
Sannan kuma ya ce wadansu kalubale da gwamnatin sa ta gada, sun kasance ne matsala a yanzu, saboda gwamnatocin baya ba su maida hankali wajen gina rayuwar al’umma ba.
Ya yi korafin yadda masu masana’antun kan su da manyan kamfanoni masu zaman kan su suka kasa samar wa dimbin jama’a ayyukan yi, ta yadda za su taimaka wajen rage yawaitar marasa aikin da ake kara samu ta dalilin yadda al’umma ke kara yawa bakatatan.
Shi kuwa shugaban gamayyar kungiyoyin, ya shawarci gwamnatin tarayya ta kara maida maida hankali wajen kara samar wa ‘yan Najeriya hanyoyin samun walwalar rayuwa, ta yadda gwamnati kuma za ta guri kara wa fetur farashi.
Sannan kuma ya yi kira da a kai karshen batun fara aiki da karin albashi da hanzari.