Shugaban Jam’iyyar PDP, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa a shekaru uku da gwamnan jihar Kogi yahaya Bello yayi yana mulkin jihar ya taka rawar ganin da jam’iyyar PDP bata iya yi ba a tsawon shekaru 16 da tayi tana mulki a jihar.
Oshiomhole ya bayyana haka ne da yake ganawa da gwamna Yahaya Bello a hedikwatar jam’iyyar APC a Abuja.
” Yahaya Bello ya cika da a jihar Kogi domin kuwa ya yi abin da ba a taba yi ba a jihar a tsawon mulkin Jam’iyyar PDP. Kada kumanta cewa tarin albashin ma’aikatan jihar da ba a iya biya ba gadarsa yayi daga gwamnatin baya, wato gwamnatin PDP.
” Sannan kuma baya ga tarin albashi da ba a biya ba, tsaro ya tabarbare a jihar da hakan yasa ake ta fama da tashin hankula a tsakanin mutanen jihar. Sai gashi yanzu komai ya lafa. Tsaro ya kankama saboda kokari da maida hankali da gwamnan yayi wajen ganin ya dawo da zaman lafiya a jihar.
Baya ga haka Oshiomhole ya ce tuni har uwar jam’iyyar ta sasanta duka wadanda basu ga maciji a tsakanin su a jam’iyyar. Sannan kuma tuni har an shirya ‘yan takarar da basuyi nasara ba a zaben fidda gwani da gwamnan jihar.
” Duka wadanda aka dakatar da wadanda suka fadi zabe a zaben fidda gwani duk sun hakura sun amince za suyi wa gwamna Bello aiki domin samun nasara a zaben gwamnan dake tafe a watan Fabrairu.