Atiku ya nemi afuwar ‘yan Najeriya, ya daina bata lokaci – Lai

0

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya yi kira ga dan takarar PDP Atiku Abubakar ya nemi afuwar ‘yan Najeriya saboda bata wa Shugaba Muhammadu Buhari lokaci da ya yi wajen kirkiro soki-burutsu a kotu da sunan daukaka kara.

Lai ya ce hakan ya kamata Atiku ya yi, maimakon sake bata lokacin sa sake garzayawa Kotun Koli.

Ranar Laraba bayan Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta yanke hukunci, daya daga cikin lauyoyin PDP ya bayyana cewa, ba su hakura ba, za su garzaya Kotun Koli.

Sannan kuma ita ma PDP din ta bayyana hukumcin a matsayin bambarakwai, kuma baunawan-burmi.

Lai ta bakin kakakin yada labaran sa Segun Adeyemi, ya ce PDP na da ‘yancin daukaka kara ko ma zuwa ina ne. “Amma dai jam’iyyar ta sani cewa wannan hakilo da kakarniyar neman sai sun koma kan mulki, wasa kawai suke yi, kuma jama’a dariya kawai su ke yi musu.

Ya ce tuni da dama ‘yan Najeriya sun gaji da PDP, tunda kuma jam’iyyar ta sha kasa, to kamata ya yi ta kakkabe keya, ta zo ta bi sahun ‘Nes Labul’ a tafi tare da ita.

Lai ya ci gaba da cewa ganin yadda dukkan alkalan biyar suka yi ittifaki wajen korar karar, hakan ya nuna cewa PDP da Atiku ba su da wata hujja, sai soki-burutsu kawai.

Ministan ya ce ai PDP da Atiku sai su gode Allah, ganin yadda kotu ba ta hukunta su ba, saboda gabatar wa kotun da hujjoji na bogi da kulle-kullen barababiyar neman karkatar da hukuncin kotu a bangaren su.

Daga nan sai ya jinjina wa alkalan kotun ganin yadda suka kashe yini guda cur su na gabatar da yanke hukunci dalla-dalla, bayan daukar tsawon kwanaki su na bibiyar kadin shari’ar.

Lai ya kuma gode wa ‘yan Najeriya saboda irin goyon bayan da suke ci gaba da bai wa gwamnatin Buhari.

Share.

game da Author