An yi garkuwa da mahaifiyar dan majalisa a Jigawa

0

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mahaifiyar tsohon dan majalisan jihar Jigawa Yahaya Muhammad, Ladi Hamza mai shekaru 75.

Yahaya ne tsohon mai ba gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru shawara kan harkokin siyasa.

Kwamishinan ‘yan sandan Najeriya Bala Senchi, ya bayyana cewa masu garkuwan sun arce da Ladi ne a gidan ta dake Danladin Gumel, Karamar hukumar Sule Tankarkar.

Sai dai kuma yace tuni har jami’an ‘Yan sanda sun fantsama cikin dazukan da ke kewaye da garin domin ceto Ladi.

Share.

game da Author