Hukumar Tsaro ta Sojoji ta bayyana korar wasu sojoji uku da aka damke cikin gungun masu garkuwa da mutane a bayan garin Maiduguri.
Kwamandan Tsara Dabarun Yakin a ‘Operation Lafiya Dole’, Olusegun Adeniyi ne bayyana haka a lokacin da ya ke damka korarrun sojojin uku a hannun hukumar ‘yan sanda a Maiduguri.
Manjo Janar Adeniyi ya ce an kama sojojin tare da wasu mutane 22 da ake zargi da sassafe, a ranar waccan Lahadi a cikin wani gini da ke bayan garin Maiduguri.
Ya kara da cewa sojojin wadanda aka kora, an turo su aiki ne a karkashin ‘Operation Lafiya Dole’, amma suka bijire, su na zuwa yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, kisa da kuma kungiyar asiri.
“ Wadannan sojoji uku na cikin batagarin da muka kama. Da farko sun yi kokarin arcewa, amma sai aka ci-dunun su, aka daure su da igiya, sabada lokacin da aka kaddamar musu babu ankwa a hannun jami’an mu.
Adeniyi ya ce a lokacin da aka kama su, ba zai yiwu a saka su cikin motar ‘yan sanda ba, saboda guduwa za su yi kuma su tayar da hankali a cikin motar.
Ya ce duk ba su da lokacin ci gaba da aiki tare da irin wadannan baragurbin jami’ai acikin sojoji. Kora ce kawai ta kamace su, kuma an kore su kamar yadda ka’idar dokar aikin soja ya tanadar.