An gano gawar Kwamandar Sojan Ruwan da ta bace a cikin rijiya

0

An tsinto gawar Kwamandar Sojan Ruwa da ta bace cikin makonni biyu da suka gabata a Kaduna.

An gano gawar ta O.O Ogundana ce a cikin wata rijiya marar zurfi, kamar yadda majiyar sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES.

Ogundana ita ce Shugabar Kwalejin ‘Yayan Sojoji da ke Jaji, Kaduna, kafin bacewar ta, wato Command Staff Secondary School, Jaji.

Ana zargin wani malamain makarantar da ta ke shugabanci ne ya kashe ta.

Cikinn makon jiya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Ogundana ta bace, a ka yi ta nema ba a gan ta ba. Sai bayan kwanaki hudu da bacewar ta, sannan aka tabbatar da cewa an neme ta, amma an rasa inda ta ke.

Ana Zargin Simon Bernard da Kashe ta

Wanda ake zargin mai suna Simon Bernard, majiya ta ce dadiron ta ne, su na neman juna.

Bernard ya amsa cewa shi ne ya kashe ta, saboda ta cire shi da shugabancin Kungiyar Iyaye Da Malaman Makaranta.

Sannan kuma akwai haushin ta yi masa alkawarin bas hi naira 2.5, amma ta kasa cikawa.

An gano gawar ta a rijiya

Hukumomin Sojoji a Jaji sun shiga neman inda za su gano Ogundana bayan bacewar ta tun ranar Litinin, 13 Ga Satumba.

Sai jiya Lahadi, 22 Ga Satumba ne aka gano gawar ta a cikin wata rijiya bayan har ta rube. An gano gawar ta a cikin leda ‘Ghana-Must-Go’, kuma a cikin rijiya.

“Da karfe 12:45 na ranar Lahadi aka gano gawar Kwamanda OO Ogundana, a Anguwan Loya, gefen hanyar jirgin kasa, cikin wata rijiya.” Haka wani babban jami’ain soja ya bayyana.

Majiyar ta ce tuni aka kama mutane uku da ake zargi na da hannu.

“Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Bernard Simon, malami ne a makarantar ta Kwalejin Jari. Sai kuma wani mai suna Ibrahim Mamman. Dukkan su na tsare ana ci gaba da bincike.”

Majiyar ta ce ana tsare da mutanen biyu ne, tare da na ukun su, wani yaron da ke yi ma ta hidima a gida, wanda shi ma ana zargin akwai rawar da ya taka, wajen bacewa ko kisan kwamandar.

“An kashe ta, aka cusa gawar ta cikin ledar ‘Ghana-must-Go’, sannan aka dauke ta aka jefa cikin rijiya a Anguwan Loya, a Jaji.”

Yadda aka kama su

Majiya ta ce an kama wadanda ake zargin a lokacin da suka yi kokarin sayar da motar ta kirar Toyota Highlander a Kaduna, bayan sun jefar da gawar ta a cikin rijiya.

“A ranar 16 Ga Satumba, Ibrahim Mamman ya tuka motar ta daga Jaji a ajiye ta Air Provost Squadron a Kaduna, bayan mai ya kare wa motar.”

“Sai ya fita waje domin ya sayo fetur, washegari ya dawo ya dauki motar.

“Yayin da ‘yan sanda suka samu labarin cewa motar samfurin Jeep SUV, ta Kwamandar Jaji ce, sai suka damke direban, suka tsare shi.

“Bayan kama direban mai suna Ibrahim Mamman, ya ce wani mutum ya ba shi motar ya sayar a Jaji.”

“Ranar 22 Ga Satumba, 2019, wajen karfe 11:30 na rana, an damke Bernard Simon, bayan kwanaki da aka shafe ya na wasan buyar kasa kama shi.

“Simon shi ne tsohon Shugaban Kungiyar Iyaye da Malaman makarantar ta Jaji.”

Majiya ta ce Bernard ya yi ikirarin kashe matar a Anguwan Loya, kusa da Jaji, a ranar 15 Ga Satumba, wajen karfe 1 na dare.

“Ya furta da kan sa cewa ya na neman ta, kuma ta yi masa alkawarin ba shi naira milyan 2.5, amma ta kasa cikawa.

“Sannan kuma sun samu sabani, saboda ta cire shi daga shugabancin Kungiyar Iyaye da Malaman Makaranta (PTA).

Har yau dai Hukumar Tsaro ta Sojojin Ruwa ba ta fitar da bayani dangane da wannan kisa ba.

Share.

game da Author