Hukumar Kula da Yanayin Tumbatsar Ruwan Sama Da Nazarin Ambaliya (NIHSA), ta bayyana cewa alamomi da yawa na nuna cewa kudancin kasar nan za ta yi fama da ambaliya musamman daga watannin Satumba zuwa Nuwamba 2019.
Babban Daraktan NIHSA Clement Nze ya tabbatar da haka ne ranar Litini a Abuja da yake yin bayani kan sakamakon binciken da hukumar ta gudanar game da ambaliyar ruwa da kasa za ta yi fama da shi bana.
Nze ya ce idan ba a manta ba a farkon daminan bana hukumar ta yi jawabi na gargadi game da ambaliyar ruwan da za a yi fama da shi amma mutane, gwamnatoci da masu ruwa da tsaki a kasar nan suka yi wa gargadin kunnen uwar shegu.
Ya ce sakamakon binciken da hukumar ta yi ya nuna cewa ruwa ba zau sauka da wuri ba amma kuma zai dauke kafa da wuri.
“ Mun kuma gano cewa tun daga ranar 26 ga watan Satumba damina zai dauke kafa a jihohin Sokoto da Katsina sannan ya gangaro zuwa jihohin dake kudancin kasarnan.
“Sai dai kuma a sassan kudancin kasarnan zai kai har zuwa watannin Nuwanba da Disamba.
“Yin kunnen uwar shegu da gargadin da mukayi da gwamnatoci, masu ruwa da tsaki da mutane a kasar nan yasa aka rika fadawa cikin hadarin ambaliyan ruwa inda ka yi ta rasa rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma kara da cewa kogin Benuwai na nan ya cika da idan ba ayi taka tsantsan ba wannan kogi ya yi ambaliya toh ko jihohi da dama zasu fada cikin halin Ka-ka-nika-yi.
Wadannan jihohi kuwa sun hada da Adamawa, Taraba, Benuwai, Katsina, Sokoto, Zamfara, Kaduna, Kwara, Bauchi, Gombe, Filato, Yobe, Kogi, Nasarawa, Anambara, Delta, Bayelsa, Edo, Legas, gun, Osun, Oyo, Abia, Cross Rivers, Barno,Jigawa,Kano,Ekiti da Oyo da Abuja.
Discussion about this post