Akalla gonaki 3000 ne da gidaje 120 suka salwanta a ambaliyar ruwa da ya afka wa garin Zugo dake karamar hukumar Guri jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na karamar hukumar, Sanusi Doro ne ya bayyana haka inda ya kara da cewa sai da aka nemi matasa suka rika cika buhuna da kasa suna toshe hanyoyin ruwan.
Ya kara da cewa wannan ambaliya da aka yi ya wanke manyen tituna da ya hada da babban titin Una-Zugobia. Hakan yasa ba a iya jigilar kaya kayan gona zuwa kasuwanni da kuma shiga gonakin.
Doro yayi kira ga Hukumar Samar da Agajin Gaggawa ta jihar da su taimaka wa mutanen da suka tafka hasara a dalilin wannan ambaliya da akayi.
Jihar Jigawa na fama da matsalar ambaliya akai-akai a duk lokaci na damuna.