Aisha Buhari ta yi kira ga kasashen Afrika dasu maida hankali wajen yaki da yaduwar Tarin Fuka

0

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da su kara maida hankali wajen ganin sun kawar da cutar tarin fuka a kasashen su.

Aisha ta ce za a samu nasarar yin haka ne idan gwamnatocin kasashe suna ware kudade masu yawa don dakile yaduwar cutar.

Idan ba a manta ba bincike ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashe 14 a duniya da wannan cuta yayi wa katutu domin binciken ya nuna cewa Najeriya ne kasa ta shida a duniya da ke fama da cutar sannan kasar ta fi yawan mutanen dake dauke da cutar a Afrika.

Bincike ya kuma nuna cewa mutane aƙalla 407,0000 ne ke kamuwa da wannan cuta a Najeriya duk shekara.

Sannan daga cikin wannan yawa kashe 25 bisa 100 ne ke iya samun magani a Najeriya.

Hakan na da nasaba ne da karancin kudade da bangaren yaki da cutar ke fama da shi saboda mafi yawan kudaden da bangaren ke amfani da su tallafi ne daga kungiyoyin bada tallafi.

Duk da haka dai Najeriya ta samu ci gaba a dakile yaduwar cutar amma aiki na nan da yawa a gaba.

Aisha ta ce a dalilin haka take kira ga gwamnatoci, masu ruwa da tsaki, bangaren masu zaman kansu, kungiyoyin kare hakin dan adam, gidajen jaridu, da sauran mutane a Afrika da su hada hannu domin ganin an samu nasarar kawar da cutar.

A karshe shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Tedros Ghabreyesus ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnati domin ganin an samu nasaran dakile cutar a kasashen Afrika.

Share.

game da Author