Ministan harkokin kasashen waje na kasar Afrika Ta kudu Naledi Pandor, ta sanar da rufe ofishin jakadancin ta dake Najeriya.
Naledi Pandor, ta ce kasar tayi haka ne zuwa a samu kwanciyar hankali a tsakanin kasashen biyu tukunna.
Pandor ta bayyana cewa kasashen biyu na tattaunawa a tsakanin su domin kawo karshen wannan matsala da ya cukuikuye kasashen biyu.
Idan ba a manta ba matasa sun fusata a jihar Akwa-Ibom inda suka cinna wa ofishin sadarwa na MTN wuta.
Matasan sun fusata ne bayan samun rahoton yadda ‘yan kasar Afrika Ta Kudu suke kashe ‘yan Najeriya a kasar su da kuma barnata musu dukiyoyi.
Wannan hare-hare da ake ta kai wa baki a kasar Afrika ta kudu ya tada wa mutanen kasar nan hankali da dama domin ba jihar Akwa-Ibom ba kawai har a jihar Legas ta dau zafi a yammacin Talata.
A jihar Legas, matasa sun kai hari babban dakin siyar da kayan masarufi na Shoprite inda sai da ‘Yan sanda suka kawo wa ma’aikata da ita kanta Shoprite din dauki.
Sai dai kuma a daidai ana yin haka ne fa kuma, sai aka samu rahoton cewa matasa sun cinna wa motar ‘Yan sanda wuta bayan ‘yan sandan sun dirka wa daya daga cikin masu zanga-zangar harsashi a ciki.
A jihar Akwa-Ibom kuwa daya daga cikin ma’aikatan ofishin MTN da aka cinna wa wuta tace bayan wuta da suka cinna wa ofishin, matasan sun wawuri na’urorin Komfuta, kudade da wayoyin mutane da suka kawo ofishin.