ZAZZABI: Maida hankali wajen yin bincike ne mafita ga kasashen duniya – WHO

0

Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa lallai sai fa kasashen duniya sun maida hanakali matuka wajen zakulo sabbin hanyoyi da matakan dakile ci gaba da yaduwar zazzabin cizon sairo da ake fama dashi a duniya, in ba haka ba kuwa ba za a kai ga ci ba.

WHO ta ce za a samu nasara a haka ne idan aka kara yawan kudaden da bangaren bincike ke samu a duniya.

A yanzu haka sashen gudanar da bincike na samun kasa da kashi daya bisa dari da haka ya yi kasa da adadin yawan kudaden da ake bukata domin gudanar da bincike.

Shugaban WHO Tedro Ghebreyesus ya yi bayyanin cewa matakan hana yaduwar cutar da ake amfani da su a yanzu haka a duniya tuni sun zama tsoffin hanyoyi.

Ghebreyesus yace lokaci ya yi da WHO tare da hadin gwiwar kungiyoyin bada tallafi su hadu domin kawo kashen wannan matsala a duniya.

Kasashen Afrika ne suka fi fama da matsalar zazzabin cizon sauro. Sannan kuma kalilan ne daga cikin su ke amfani da gidan sairo da kuma yi wa gidajen su feshi.

Ghebreyesus yace ya zama dole a mike haikan domin tsaro sabbin hanyoyi domin dakile wannan cuta da tunda wuri.

Share.

game da Author