Kotun dake sauraren karrakin zaben majalisar dattawa a Kaduna ta yi watsi da karar da Sanata Shehu Sani ya shigar gabanta yana kalubalantar zaben Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC da aka yi bayan zaben 2019.
Idan ba a manta ba, hukumar zabe ta bayyana Uba Sani a matsayin wanda ya yi nasara a zaben sanatan a watan Fabrairun 2019.
Bayan bayyana sakamakon zaben ne, Shehu Sani na jam’iyyar PRP yayi watsi da wannan sakamako inda ya ce an tafka magudi a kananan hukumomin dake karkashin wannan shiyya da akayi zabe.
Alkalin kotun ya bayyana cewa wannan kara bata da nagarta, a dalilin haka ya wancakalar da ita.
Bayan an tashi zaman kotu sai lauyan Uba Sani, Frank Igbe, ya bayyana cewa wannan hukunci yayi masu dadi matuka. Ya ce dama abinda suke tsammanin zai faru kenan domin sam karar bata da wani tasiri.
Shima wanda ya zo na biyu a zaben Lawal Adamu na jam’iyyar PDP da ya shigar da kara yana kalubalantar wannan sakamako da aka bayyana Uba Sani ne ya lashe zaben. Adamu zai san matsayin sa ranar 24 ga wannan watan haka shima Barnabas Bantex na APC zai san sakamokon karar da ya shigar ranar 26 ga wata.
Discussion about this post