Za a fara koyar da darussan sarrafa magungunan gargajiyya a jami’o’in kasar nan -Ma’aikatar kiwon lafiya

0

Shugaban hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) Mojisola Adeyeye ta yi kira ga masu sarrafa magungunan gargajiya da su hada hannu da kamfanonin dake sarrafa magungunan zamani a kasarnan domin ci gaban fannin.

Mojosola ta fadi haka ne a taron baje kolin magungunan gargajiya wanda kungiyar masu sarrafa magungunan gargajiya da ma’aikatar kiwon lafiya suka shirya.

A jawabin da ta yi a wajen taron Mojisola ta ce matsalolin dake ci wa fannin hada magungunan gargajiyya tuwo a kwarya sun hada da rashin yin bincike, rashin hada hannu da bangaren masu gudanar da bincike na kimiya da fasaha domin tabbatar da ingancin magungunan.

Ta ce wadannan matsaloli sun hana wannan sashe samun ci gaba.

Mojisola ta ce tabas magungunan gargajiya na taimakawa wajen kawar da cututtuka amma dai camfin da ake yi wai baya yin lahani a jiki shine ya kamata a maida hankali a kai sannan a sanarwa mutane cewa lallai sai fa an bi a hankali wajen amfani da ire-iren wasannan magunguna.

“Magungunan gargajiyya na yin lahani a jikin mutum idan ba a yi amfani da shi yadda ya kamata ba.

“A dalilin haka muke kira ga masu sarrafa magungunan gargajiya kan hada hannu da masu yin bincike na kimiya da fasaha domin tabbatar da ingancin magungunan da zasu rika amfani da su.

Ta kuma ce hukumar NAFDAC na sashen da ta bude domin tantance ingancin magungunan gargajiyyar da ake sarrafawa a kasar nan sannan ta yi kira ga duk masu sarrafa magungunan gargajiyya da su yi rajista da wannan sashe bangare a hukumar.

A karshe babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya Abdullahi Abdulaziz ya bayyana cewa gwamnati na kokarin ganin jami’o’in kasar nan na koyar da darussan sarrafa magungunan gargajiyya.

Share.

game da Author