Gwamnatin jihar Gombe ta ciyo bashin Naira biliyan 3.4 daga bankin duniya domin shirin ta na yaki da kawar da yunwa a jihar.
Jami’in kula da hidimomi na kasa na cibiyar kawar da yunwa a Najeriya (ANRiN) Kamil Shoretire ya sanar da haka da yake hira da manema labarai a taron tattaunawa da tsaro shirye-shirye domin kawo karshen yunwa a jihar.
“Sakamakon binciken da cibiyar NDHS ta gudanar ya nuna cewa yara miliyan 15 ne aka tabbatar sannan ya nuna suna fama da matsalar Yunwa a jihar.
” Burin mu shine rage yawan yara kanana ‘yan kasa da shekara biyar dake fama da yunwa a kasar nan.”
Shoretire ya ce wannan aiki zai fi maida hankaline ne wajen inganta kiwon lafiyar mata gaba ki daya, da yara kanana da kuma mata masu shayarwa.
A karshe jami’in hukumar reshen jihar Gombe Suleman Mamman ya bayyana cewa bisa ga yarjejeniyyar samun wannan kudi gwamnatin jihar zata rika biyan karin akalla kashi 0.6 a na kudaden da ta karba a hankali-a hankali har zuwa ta gama biya.
Mamman yace babban dalilin karban wannan bashi shine domin kawar da yunwa a jikin musamman yara kanana a jihar ganin cewa adadin yawan yaran dake fama da yunwa a jihar ya karu daga kashi 46.6 a 2018 zuwa kashi 50 a 2019.
Discussion about this post