‘Yar shekara 14 ta yi karyan yin garkuwa da ita don ta ziyarci saurayinta a wani gari

0

Wata ‘yan shekara 14 ta shirga wa mahaifinta karya cewa wai masu garkuwa sun arce da ita.

Bayan mahaifinta ya samu wannan sanarwa sai ya garzaya ofishin ‘yan sanda inda ya mika kukan sa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu Ebere Amaraizu, ya ce da suka samu wannan kuka daga mahaifin wannan yarinya da ta bace sai suka fantsama aiki cikin gaggawa.

” Ba a dade da fara bincike ba sai muka gano ashe ita wannan yarinya ‘yar shekara 14 ta gudu ne zuwa garin saurayinta domin wai tana kewarsa. Da ita da wannan saurayi nata ajin su daya a sakandare (SS1) a makaranta. Sai dai kuma a wannan dogon hutu da suke yi ta kasa hakuri adawo makaranta saboda kewar sa shine ta waske abinta zuwa can garin saurayin domin ta ganshi na dan kwanaki.

Yanzu dai an dawo da wannan yarinya zuwa gidan mahaifan ta sannan ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike akai.

Ita wannan yarinya mai suna Kosisochukwu Anioma, ta ce ta kasa hakuri ne a dawo makaranta. Shi ko mahaifinta Frank Anioma da hamshakin dan siyasa ne a jihar Enugu ya ce hankalin su a gida yayi matukar tashi.

Share.

game da Author